Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 58: Dauda da Goliath

Labari na 58: Dauda da Goliath

FILISTIYAWA suka sake zuwa su yaƙi Isra’ila. Yanzu ’yan’uwan Dauda uku suna cikin sojojin Saul. Sai wata rana Jesse ya gaya wa Dauda: ‘Ka ɗauki gurasa da kuma hatsi ka kai wa ’yan’uwanka. Ka kuma duba yaya suke.’

Goliath

Sa’ad da Dauda ya isa sansani sojojin ya ruga zuwa bakin daga ya nemi ’yan’uwansa. Gwarzon Filistiyawa Goliath ya fito ya yi wa Isra’ilawa ba’a. Yana yi wa Isra’ilawa haka dare da rana har na kwanaki 40. Yana yin kururuwa: ‘Ku zaɓi ɗaya daga cikinku ya yaƙe ni. Idan ya yi nasara ya kashe ni, za mu zama bayinku. Amma idan na yi nasara na kashe shi, za ku zama bayinmu. Na ƙalubalance ku ku fito da mutumin da zai yi faɗa da ni.’

Dauda ya tambayi wasu sojoji: ‘Menene mutumin da ya kashe wannan Bafilisti kuma fid da Isra’ila daga wannan kunya zai samu?’

‘Saul zai ba mutumin arziki mai yawa,’ in ji sojojin. ‘Kuma zai aura masa ’yarsa.’

Amma dukan Isra’ilawa suna tsoron Goliath domin ƙato ne sosai. Ya fi ƙafa 9 tsawo, kuma yana da wani soja da yake riƙe masa garkuwansa.

Wasu sojoji suka je suka gaya wa Sarki Saul cewa Dauda yana so ya yi faɗa da Goliath. Amma Saul ya gaya wa Dauda: ‘Ba za ka iya yin faɗa da wannan Bafilisti ba. Domin yaro ne kai, kuma duka rayuwarsa shi soja ne.’ Dauda ya amsa: ‘Na kashe wata dabbar daji da zaki da suka kama tumakin babana. Kuma wannan Bafilisti zai zama kamar ɗaya daga cikinsu. Kuma Jehobah zai taimake ni.’ Saboda haka Saul ya ce: ‘Ka tafi Jehobah ya kasance tare da kai.’

Dauda ya tafi bakin wani rafi ya samo duwatsu biyar masu santsi, ya zuba su cikin jakarsa. Sai ya ɗauki majajjawarsa ya fita ya tari gwarzon. Sa’ad da Goliath ya gan shi, ya yi mamaki. Yana tsammanin zai yi masa sauƙi ya kashe Dauda.

Dauda yana jefa dutse

‘Ka zo,’ in ji Goliath, ‘zan ba da namanka ga tsuntsaye su ci.’ Amma Dauda ya ce: ‘Kana zuwa wurina da takobi da mashi da kunkeli, amma ni na zo wurinka cikin sunan Jehobah. Yau Jehobah za ya bashe ka cikin hannuna kuma zan buge ka har ƙasa.’

Sai Dauda ya ruga zuwa wurin Goliath. Ya ɗauki dutse daga cikin jakarsa, ya saka cikin majajjawarsa, ya harba da dukan ƙarfinsa. Dutsen ya tafi kai tsaye ya bugi goshin Goliath, Goliath ya faɗi ya mutu! Sa’ad da Filistiyawa suka ga gwarzonsu ya mutu, dukansu suka ruga da gudu. Isra’ilawa suka bi su suka ci su a yaƙi.

1 Samuila 17:1-54.Tambayoyi

 • Wane ƙalubale ne Goliath ya yi wa rundunar Isra’ilawa?
 • Yaya girman Goliath yake, wane lada ne Sarki Saul ya yi alkawari zai ba mutum da ya kashe Goliath?
 • Menene Dauda ya ce sa’ad da Saul ya gaya masa ba zai iya faɗa da Goliath ba domin shi ɗan yaro ne?
 • Ta amsa da ya ba Goliath, ta yaya ne Dauda ya nuna ya dogara ga Jehobah?
 • Kamar yadda ka gani a wannan hoton, da menene Dauda ya kashe Goliath, kuma menene ya faru da Filistiyawa bayan haka?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta 1 Samuila 17:1-54.

  Me ya sa Dauda ba ya jin tsoro, kuma ta yaya za mu yi koyi da gaba gaɗinsa? (1 Sam. 17:37, 45; Afis. 6:10, 11)

  Me ya sa ya kamata Kiristoci su guje wa halin gasa kamar na Goliath sa’ad da suke wasanni ko kuma nishaɗi? (1 Sam. 17:8; Gal. 5:26; 1 Tim. 4:8)

  Ta yaya kalmomin Dauda suka nuna yana da bangaskiya cewa Allah zai goyi bayansa? (1 Sam. 17:45-47; 2 Laba. 20:15)

  Maimakon kwatanta faɗa tsakanin abokan gaba biyu da rundunarsu, ta yaya wannan labarin ya nuna cewa yaƙin ainihi tsakanin allolin ƙarya ne da Jehobah Allah na gaskiya? (1 Sam. 17:43, 46, 47)

  Ta yaya shafaffu da suka rage suka yi koyi da misalin Dauda wajen dogara ga Jehobah? (1 Sam. 17:37; Irm. 1:17-19; R. Yoh. 12:17)