Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 9: Nuhu Ya Gina Jirgi

Labari na 9: Nuhu Ya Gina Jirgi
Mutane suna yi wa Nuhu dariya

NUHU yana da mata da ’ya’ya uku. Sunayen ’ya’yansa su ne Shem, Ham, da Japheth. Kuma kowane cikin waɗannan yara yana da matarsa. Wato, mutane takwas ke nan a iyalin Nuhu.

Allah ya ce wa Nuhu ya yi wani abin mamaki. Ya ce masa ya gina wani babban jirgi. Wannan jirgin zai kasance babba ne kamar jirgin ruwa, amma yana kama da babban akwati ne. ‘Ka gina shi mai hawa uku’ in ji Allah, kuma ‘ka gina ɗakuna a ciki.’ Waɗannan ɗakuna na Nuhu da iyalinsa ne, da kuma dabbobi da kuma abincinsu duka.

Allah kuma ya gaya wa Nuhu ya liƙe jirgin domin kada ruwa ta shiga ciki. Allah ya ce: ‘Zan tura ruwa mai yawa ta halaka dukan duniya. Dukan wanda ba ya cikin jirgin zai mutu.’

Nuhu da ’ya’yansa suka yi wa Jehobah biyayya suka fara gina jirgin. Amma sauran mutane suka yi dariya. Suka ci gaba da yin mugunta. Babu wanda ya gaskata Nuhu sa’ad da ya gaya musu abin da Allah zai yi.

Iyalin Nuhu suna saka dabbobi da abinci a cikin jirgin

Gina jirgin ya ɗauki lokaci mai tsawo domin yana da girma sosai. A ƙarshe bayan shekaru masu yawa, aka gama ginin. Sai Allah ya gaya wa Nuhu ya saka dabbobin cikin jirgin. Allah ya ce ya saka wasu ire-iren dabbobi biyu, na mace da namiji. Amma wasu irin dabbobi, Allah ya gaya wa Nuhu ya saka su bakwai. Allah ya gaya wa Nuhu ya saka dukan ire-iren tsuntsaye. Nuhu ya yi daidai abin da Allah ya gaya masa.

Daga baya, Nuhu da iyalinsa ma suka shiga cikin jirgin. Sa’an nan sai Allah ya rufe ƙofar. Nuhu da iyalinsa suka yi jira a cikin jirgin. Ka yi tunanin kana tare da su a cikin jirgin kana jira. Da gaske ne tsufana za ta zo kamar yadda Allah ya ce?

Farawa 6:9-22; 7:1-9.Tambayoyi

 • Mutane nawa ne suke cikin iyalin Nuhu, kuma menene sunayen ’ya’yansa uku?
 • Wane abin mamaki ne Allah ya ce wa Nuhu ya yi, kuma me ya sa?
 • Menene maƙwabtan Nuhu suka yi sa’ad da ya gaya musu game da jirgin?
 • Menene Allah ya gaya wa Nuhu ya yi da dabbobi?
 • Bayan da Allah ya rufe ƙofar jirgin, menene Nuhu da iyalinsa suka yi?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Farawa 6:9-22.

  Menene ya sa Nuhu ya kasance fitaccen bawan Jehobah? (Far. 6:9, 22)

  Yaya Jehobah ya ji game da muguntar da ake yi, kuma ta yaya wannan ya kamata ya shafi irin nishaɗi da muke so? (Far. 6:11, 12; Zab. 11:5)

  Ta yaya za mu yi koyi da Nuhu sa’ad da muka sami ja-gora ta wurin ƙungiyar Jehobah? (Far. 6:22; 1 Yoh. 5: 3)

 • Ka karanta Farawa 7:1-9.

  Ta yaya ne yadda Jehobah ya ɗauki Nuhu mutum ajizai mai adalci zai ƙarfafa mu a yau? (Far. 7:1; Mis. 10:16; Isha. 26:7)