DUBI duniya a nan! Yadda kome yake da yau! Dubi ciyayi da itatuwa, furanni da kuma dukan waɗannan dabbobi. Za ka iya nuna giwaye da kuma zakuna?

Dabbobi a lambun Adnin

Ta yaya aka sami wannan lambu mai kyau? To, bari mu ga yadda Allah ya shirya duniya dominmu.

Da farko, Allah ya rufe ƙasa da ciyayi. Sai ya yi dukan ire-iren ƙananan tsiro da shuka da itatuwa. Waɗannan abubuwa ne suka sa duniya ta yi kyau. Amma amfanin su ya fi kawai su kyawanta duniya. Yawancinsu kuma suna ba mu abinci mai daɗi.

Daga baya Allah ya halicci kifaye su yi iyo cikin ruwa, tsuntsaye kuma su yi firiya a sama. Ya kuma halicci karnuka, kyanwoyi, da dawakai, manyan dabbobi da kuma ƙananan dabbobi. Waɗanne dabbobi ne suke kusa da gidanku? Bai kamata ba ne mu yi farin ciki cewa Allah ya halicci dukan wannan dominmu?

A ƙarshe, Allah ya mai da wani ɓangaren duniya wuri na musamman. Ya kira wannan wurin lambun Adnin. Wuri ne mai kyaun gaske. Kome game da wurin kyakkyawa ne. Kuma Allah yana so dukan duniya ta zama kamar wannan lambun da ya yi.

Amma ka sake kallon hoton wannan lambun. Ka san abin da Allah ya ga cewa babu a lambun? Bari mu gani.

Farawa 1:11-25; 2:8, 9.Tambayoyi

 • Ta yaya Allah ya shirya duniya domin ta zama gidanmu?
 • Ka kwatanta ire-iren dabbobin da Allah ya halitta. (Dubi hoto.)
 • Me ya sa lambun Adnin wuri ne na musamman?
 • Menene Allah yake so dukan duniya ta zama?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Farawa 1:11-25.

  Menene Allah ya halitta a rana ta uku ta halitta? (Far. 1:12)

  Menene ya faru a rana ta huɗu ta halitta? (Far. 1:16)

  Waɗanne irin dabbobi ne Allah ya halitta a rana ta biyar da ta shida? (Far. 1:20, 21, 25)

 • Ka karanta Farawa 2:8, 9.

  Waɗanne itatuwa ne biyu na musamman Allah ya saka a lambun, kuma alamar menene ne su?