Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 1: Allah Ya Fara Halittar Abubuwa

Labari na 1: Allah Ya Fara Halittar Abubuwa

DUKAN abubuwa masu kyau da muke da su sun zo daga wurin Allah ne. Shi ya halicci rana don ta ba mu haske da rana, wata kuma da taurari don haske daddare. Sa’an nan Allah ya yi duniya domin mu zauna cikinta.

Amma rana, wata da taurari da kuma duniya ba sune Allah ya fara halitta ba. Ka san abin da ya fara halitta? Da farko Allah ya halicci halittu kamarsa. Ba za mu iya ganinsu ba, kamar yadda ba za mu iya ganin Allah ba. An kira su mala’iku a cikin Littafi Mai Tsarki. Allah ya halicci mala’iku domin su zauna a sama tare da shi.

Mala’ikan da Allah ya fara halitta na musamman ne. Shi ne ɗan farin Allah, kuma ya yi aiki tare da Ubansa. Ya taimaki Allah wajen halittar dukan sauran abubuwa. Ya taimaki Allah wajen halittar rana, wata da kumfa taurari da kuma duniyarmu.

Yaya duniya take a lokacin? Da farko babu wanda zai iya zama a duniya. Babu wani abu sai wata babbar teku da ta rufe ƙasa. Amma Allah yana so mutane su zauna a duniya. Sai ya fara shirya mana abubuwa. Menene ya yi?

To, da farko dai, duniya tana bukatar haske. Saboda haka Allah ya sa hasken rana ta haskaka duniya. Kuma ya sa ya kasance za a sami dare da rana. Bayan haka Allah ya sa ƙasa ta fito daga cikin tekun.

Da farko, babu kome a kan ƙasar. Ƙasar ta yi kama da hoton da kake gani a nan. Babu furanni ko itatuwa ko kuwa dabbobi. Babu ko kifi guda ɗaya a cikin tekun. Allah yana da babban aiki kafin ya mai da duniya ta zama wuri mai kyau domin dabbobi da kuma mutane su zauna cikinta.

Irmiya 10:12; Kolosiyawa 1:15-17; Farawa 1:1-10.

Ƙasar da babu kome


Tambayoyi

 • Daga ina dukan abubuwa masu kyau suka fito, kuma za ka iya ba da misali?
 • Menene Allah ya halitta da farko?
 • Me ya sa mala’ika da Allah ya halitta da farko mala’ika ne na musamman?
 • Ka kwatanta yadda duniya take da farko. (Dubi hoto.)
 • Ta yaya Allah ya fara shirya duniya domin dabbobi da kuma mutane?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Irmiya 10:12.

  Waɗanne halayen Allah ne suka bayyana ta wajen abubuwan da ya halitta? (Ish. 40:26; Rom. 11:33)

 • Ka karanta Kolossiyawa 1:15-17.

  Wane abu Yesu ya yi a lokacin halitta, kuma ta yaya wannan ya kamata ya shafi yadda muka ɗauka shi? (Kol. 1:15-17)

 • Ka karanta Farawa 1:1-10.

  Wanene ya halicci duniya? (Far. 1:1)

  Menene ya faru a ranar farko ta halitta? (Far. 1:3-5)

  Ka kwatanta abin da ya faru a rana ta biyu ta halitta. (Far. 1:7, 8)