Yesu yana magana da yara

WANNAN littafi ne na labarun da suka faru da gaske. An ɗauko su ne daga littafi mafi girma a duniya, Littafi Mai Tsarki. Labaran sun ba da tarihin duniya ne daga lokacin da Allah ya fara halitta zuwa zamanin yau. Sun ba da labarin abin da Allah ya yi alkawari zai yi a nan gaba ma.

Wannan littafin yana ba ka fahimi ne game da abin da Littafi Mai Tsarki ya ƙunsa. Ya ba da labari game da mutanen Littafi Mai Tsarki da kuma abubuwan da suka yi. Ya kuma nuna bege mai girma na rai madawwami a aljanna a duniya da Allah ya ba mutane.

Da akwai labarai 116 a wannan littafin. An raba su zuwa sashe takwas. Shafin da ke farkon kowane sashe ya ba da ɗan labari game da abin da ke wannan sashen. Labaran sun bayyana ne bisa yadda suka faru cikin tarihi. Wannan zai taimaka maka ka fahimci lokacin da abubuwa suka faru cikin tarihi.

An ba da labarin cikin harshe mai sauƙi. Yara da yawa za su iya karanta shi da kansu. Iyaye za su yi farin cikin gani cewa yara ƙanana za su so a karanta musu wannan labarai sau da yawa. Za ka ga cewa wannan littafin yana ɗauke da abin da yara da manya za su yi marmarinsa.

An rubuta inda aka ɗauko labaran a ƙarshen kowane labari. Ana ƙarfafa ka ka karanta waɗannan ɓangare na Littafi Mai Tsarki inda aka ɗauko labaran.

An sauƙaƙa ƙaulin Littafi Mai Tsarki da aka yi a wannan littafi. An furta su ne a harshe mai sauƙi saboda yara su fahimci abin da ake faɗa. A ƙarshen labarin an nuna inda aka ɗauko labarin cikin.