KA SAN abin da wannan ƙaramar yarinya da abokananta suke karantawa? Hakika, wannan littafin ne da kake karantawa, Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki. Kuma suna karanta labarin da kake karantawa ne, “Yadda Za Mu Rayu Har Abada.”

Yaro yana karatu

Ka san abin da suke koya? Da farko, cewa muna bukatar mu koyi game da Jehobah da kuma Ɗansa Yesu idan muna so mu rayu har abada. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Wannan shi ne hanyar rayuwa har abada. Ka koyi game da Allah na gaskiya, da kuma Ɗan da ya aiko duniya, Yesu Kristi.’

Ta yaya za mu koyi game da Jehobah Allah da kuma Ɗansa Yesu? Hanya ɗaya ita ce ta karanta Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki daga farko zuwa ƙarshensa. Ya gaya mana game da Jehobah da kuma Yesu, ko ba haka ba ne? Kuma ya gaya mana game da abubuwa da suka yi da kuma waɗanda za su yi. Amma muna bukatar mu yi wani abu kuma ban da karanta wannan littafin.

Littafi Mai Tsarki

Ka ga wannan littafin da yake ajiye a ƙasa? Littafi Mai Tsarki ne. Ka ce wani ya karanta maka inda aka ɗauko waɗannan labarun a Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki ya ba mu cikakken bayani da muke bukata domin mu bauta wa Jehobah a hanyar da take daidai kuma mu sami rai madawwami. Saboda haka ya kamata karatun Littafi Mai Tsarki ya zama jikinmu.

Amma muna bukatar mu yi wani abu kuma ban da koya game da Jehobah Allah da kuma Yesu Kristi. Za mu iya saninsu sosai amma kuma ba za mu sami rai madawwami ba. Ka san abin da ya kamata mu yi kuma?

Muna bukatar mu yi abubuwa da muka koya. Ka tuna Yahuda Iskariyoti? Yana ɗaya daga cikin manzanni 12 da Yesu ya zaɓa. Yahuda yana da sani sosai game da Jehobah da Yesu. Amma me ya same shi? Bayan ɗan lokaci ya zama mai sonkai, ya bashe da Yesu ga abokanan gabansa domin tsaba 30 na azurfa. Saboda haka Yahuda ba zai sami rai madawwami ba.

Ka tuna Gahazi mutumin da muka koya game da shi a Labari na 69? Yana so ya sami kayaki da kuma kuɗi da ba na shi ba. Saboda haka ya yi ƙarya domin ya sami waɗannan abubuwa. Amma Jehobah ya yi masa horo. Kuma zai yi mana horo idan ba mu bi dokokinsa ba.

Amma da akwai mutanen kirki da suka bauta wa Jehobah da aminci. Muna so mu zama kamarsu, ko ba haka ba? Sama’ila misali ne mai kyau da za mu bi. Ka tuna kamar yadda muka gani a Labari 55, yana ɗan shekara huɗu ko biyar sa’ad da ya fara bauta wa Jehobah a mazauni. Ko nawa shekarunka ba ka yi ƙarami ba sosai ka bauta wa Jehobah.

Hakika, dukanmu muna so mu bi Yesu Kristi. Har sa’ad da yake yaro ma, kamar yadda muka gani a >Labari na 87, ya kasance a cikin haikali yana magana da wasu game da Ubansa na samaniya. Ya kamata mu bi misalinsa. Bari mu gaya wa mutane da yawa game da Jehobah Allahnmu da Ɗansa, Yesu Kristi. Idan mun yi waɗannan abubuwa, za mu iya rayuwa har abada cikin sabuwar aljanna ta Allah a duniya.

Yohanna 17:3; Zabura 145:1-21.Tambayoyi

 • Menene ya kamata mu sani idan za mu rayu har abada?
 • Ta yaya za mu koya game da Jehobah Allah da Yesu, yadda ƙaramar yariyar nan da abokanta suka nuna a wannan hoton?
 • Wane littafi ne kuma ka gani a wannan hoton, me ya sa ya kamata mu karanta shi koyaushe?
 • Ban da koya game da Jehobah da Yesu, menene kuma ake bukata don a sami rai na har abada?
 • Wane darassi muka koya daga Labari na 69?
 • Menene misali mai kyau na yaro Sama’ila a Labari na 55 ya nuna?
 • Ta yaya za mu bi misalin Yesu Kristi, idan muka yi hakan, menene za mu iya yi nan gaba?

Ƙarin tambayoyi

 • .Ka karanta Yohanna 17:3.

  Ta yaya Nassosi ya nuna cewa samun cikakken sani na Jehobah Allah da Yesu Kristi ba haddace gaskiya ba ne kawai? (Mat. 7:21; Yaƙ. 2:18-20; 1 Yoh. 2:17)

 • Ka karanta Zabura 145:1-21.

  Waɗanne dalilai ne muke da su na bauta wa Jehobah? (Zab. 145:8-11; R. Yoh. 4:11)

  Ta yaya Jehobah “mai-alheri ne ga dukan mutane,” kuma ta yaya wannan ya kamata ya sa mu matsa kusa sosai da shi? (Zab. 145:9; Mat. 5:43-45)

  Idan muna ƙaunar Jehobah sosai, menene wannan zai motsa mu mu yi? (Zab. 119:171, 172, 175; 145:11, 12, 21)