Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Sashe na 8: Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Faɗa Suna Faruwa

Sashe na 8: Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Faɗa Suna Faruwa

Ban da ba da labarin abin da suka faru a dā, Littafi Mai Tsarki yana faɗan kuma abin da zai faru a nan gaba. Mutane ba za su iya faɗin abin da zai faru a nan gaba ba. Shi ya sa muka sani cewa Littafi Mai Tsarki daga Allah ne. Menene Littafi Mai Tsarki ya ce zai faru a nan gaba?

Ya faɗi game da babban yaƙi na Allah. A wannan yaƙin Allah zai kawar da dukan mugunta da kuma miyagun mutane daga duniya, amma zai kāre waɗanda suke bauta masa. Sarki da Allah ya naɗa, Yesu Kristi, zai tabbata cewa bayin Allah sun sami salama da farin ciki, kuma ba za su sake yin rashin lafiya ba ko kuma su mutu.

Za mu yi farin ciki cewa Allah zai yi aljanna a duniya, ko ba haka ba? Dole ne mu yi wani abu idan muna so mu zauna a cikin wannan aljanna. A cikin labarin ƙarshen na wannan littafin za mu koyi abin da dole ne mu yi domin mu more abubuwa masu ban sha’awa da Allah ya ajiye wa waɗanda suka bauta masa. Saboda haka ka karanta SASHE NA 8 domin ka fahimci abin da Littafi Mai Tsarki ya ce zai faru a nan gaba.

Hoton aljanna