Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Labari na 111: Yaro da Ya Yi Barci

Labari na 111: Yaro da Ya Yi Barci

WAI! WAI! Menene yake faruwa a nan? Yaron da yake kwance a ƙasa ya ji rauni ne sosai? Dubi, Bulus yana cikin mutanen da suke fitowa daga cikin wannan gidan! Ka ga Timothawus yana tare da shi? Shin yaron ya faɗi ne ta taga?

Bulus yana zuwa ya ta da Aftikos

Hakika, abin da ya faru ke nan. Bulus yana ba da jawabi ga almajirai a Taruwasa. Ya sani cewa ba zai gansu ba na dogon lokaci domin washegari zai shiga jirgin ruwa ya tafi. Saboda haka ya ci gaba da jawabi har tsakar dare.

Wannan yaron mai suna Aftikos yana zaune a kan taga, sai barci ya kwashe shi. Sai ya faɗi daga bene mai hawa uku zuwa ƙasa! Saboda haka ka ga mutanen sun damu. Sa’ad da mutanen suka ɗauki yaron kamar yadda suka yi zato ne. Ya mutu!

Sa’ad da Bulus ya ga cewa yaron ya mutu, sai ya kwanta a kansa ya rungume shi. Sai ya ce: ‘Kada ku damu. Zai sami lafiya!’ Kuma haka ya faru! Mu’ujiza ce! Bulus ya tashe shi! Jama’a suka yi ta murna.

Dukan su suka koma benen suka ci abinci. Bulus ya ci gaba da jawabi har gari ya waye. Amma mun tabbata cewa Aftikos bai yi barci ba kuma! Sai Bulus, Timothawus da waɗanda suke tafiya tare da su suka shiga cikin jirgin ruwa. Ka san inda za su tafi?

Bulus ya gama tafiyarsa ta uku ta wa’azi, yana kan hanyarsa ta komawa gida. A wannan tafiyar Bulus ya yi shekara uku a birnin Afisa. Wannan tafiya ta fi ta biyu tsawo.

Bayan ya bar Taruwasa, jirgin ya tsaya a Militus na ɗan lokaci. Tun da Afisa ba shi da nisa, Bulus ya aika aka kira dattawan ikilisiyar su zo Militus saboda ya yi musu jawabi na ƙarshe. Sa’ad da lokaci ya yi da jirgin zai tashi, suka yi baƙin cikin tafiyar Bulus!

A ƙarshe jirgin ya isa Kaisariya. Sa’ad da Bulus yana zaune a gidan almajiri Filibbus annabi Agabus ya yi ma Bulus gargaɗi. Ya ce za a jefa Bulus cikin kurkuku sa’ad da ya je Urushalima. Kuma hakan ya faru. Bayan da ya yi shekara biyu a cikin kurkuku a Kaisariya, aka aika da Bulus zuwa Roma don a yi masa shari’a a gaban Kaisar sarkin Roma. Bari mu ga abin da ya faru a kan hanyarsa ta zuwa Roma.

Ayukan Manzanni 19 zuwa 26.Tambayoyi

 • A wannan hoton, wane yaro ne yake kwanciya a ƙasa, menene ya faru da shi?
 • Menene Bulus ya yi sa’ad da ya ga cewa yaron ya mutu?
 • Ina ne Bulus, Timothawus, da waɗanda suke tafiya da su suke zuwa, kuma menene ya faru sa’ad da suka tsaya a Militus?
 • Wane kashedi ne annabi Agabus ya ba Bulus, kuma yaya abin da annabin ya faɗa ya faru?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta A. M. 20:7-38.

  Ta yaya za mu zama “kuɓutace ne daga jinin dukan mutane,” bisa ga kalmomin Bulus da ke A. M. 20:26, 27? (Ezek. 33:8; A. M. 18:6, 7)

  Me ya sa ya kamata dattawa su ‘riƙe amintacciyar magana’ sa’ad da suke koyarwa? (A. M. 20:17, 29, 30; Tit. 1:7-9; 2 Tim. 1:13)

 • Ka karanta A. M. 26:24-32.

  Ta yaya Bulus ya yi amfani da zama ɗan Roma wajen cika aikin wa’azi da Yesu ya ba shi? (A. M. 9:15; 16:37, 38; 25:11, 12; 26:32; Luk 21:12, 13)