Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 110: Timothawus, Sabon Mataimakin Bulus

Labari na 110: Timothawus, Sabon Mataimakin Bulus

WANNAN saurayi da kake gani tare manzo Bulus Timothawus ne. Timothawus yana tare da iyayensa a Listra. Sunan mamarsa Afiniki kakarsa kuma sunanta Lois.

Wannan ziyarar Bulus na uku ke nan zuwa Listra. Kusan shekara ɗaya da ya shige, Bulus da Barnaba sun zo nan a tafiye-tafiyensu na wa’azi. Yanzu Bulus ya sake zuwa da abokinsa Sila.

Timothawus da Bulus

Ka san abin da Bulus yake gaya wa Timothawus? ‘Za ka so ka bi ni da Sila?’ ya tambaye shi. ‘Za ka taimaka mana wajen yi wa wasu mutanen ƙasashe masu nisa wa’azi.’

‘E,’ in ji Timothawus, ‘Zan so in bi ku.’ Ba da daɗewa ba bayan haka Timothawus ya bar iyayensa ya bi Bulus da Sila. Amma kafin mu koyi game da tafiye-tafiyensu bari mu ga abin da ya faru da Bulus. Kusan shekara 17 ke nan tun da Yesu ya bayyana masa a kan hanyarsa ta zuwa Dimasƙa.

Ka tuna Bulus ya je Dimasƙa ne domin ya azabtar da almajiran Yesu, amma yanzu shi ma almajiri ne! Daga baya wasu abokan gaba suka ƙulla su kashe Bulus domin ba sa son koyarwarsa game da Yesu. Amma almajiran suka taimaki Bulus ya gudu. Suka saka Bulus cikin kwando suka sauke shi a bayan ganuwar birnin.

Bayan haka Bulus ya je wa’azi a Antakiya. A nan ne aka kira mabiyan Yesu Kiristoci da farko. Bulus da Barnaba suka fita daga Antakiya zuwa wa’azi a wasu ƙasashe masu nisa. Ɗaya daga cikin biranen da suka ziyarta ita ce Listra, garinsu Timothawus.

Yanzu bayan kusa shekara ɗaya, Bulus ya sake komawa Listra a zuwansa ta biyu. Sa’ad da Timothawus ya bi Bulus da Sila, ka san inda suka je? Ka dubi wannan taswira bari mu ga wasu wuraren.

Da farko suka je birni na kusa Ikoniya, sai birni na biyu wato Antakiya. Bayan nan suka tafi Taruwasa, sai suka wuce zuwa Filibbi, Tassalunika da Biriya. Ka ga inda Atina take a taswira? Bulus ya yi wa’azi a nan ma. Bayan nan sun yi shekara ɗaya da rabi suna wa’azi a Koranti. A ƙarshe suka ɗan tsaya a Afisa. Sai suka koma Kaisariya a cikin jirgin ruwa, suka wuce zuwa Antakiya inda Bulus yake da zama.

Ta haka Timothawus ya yi tafiyar ɗarurruwan mil yana taimakon Bulus wajen wa’azin “bishara” da haka suka kafa ikilisiyoyin Kirista da yawa. Sa’ad da ka girma, za ka so ka zama bawan Allah mai aminci kamar Timothawus?

Ayukan Manzanni 9:19-30; 11:19-26; surori 13 zuwa 17; 18:22.

Taswira

1. Roma; 2. Malta ; 3. Biriya; 4. Tassalunika; 5. Koranti; 6. Filibi; 7. Atina; 8. Karita; 9. Taruwasa; 10. Afisa; 11. Militus; 12. Kolosi; 13. Antakiya; 14. Ikoniya; 15. Listira; 16. Kubrus; 17. Antakiya; 18. Kaisariya; 19. Yafa; 20. Dimasƙa; 21. Urushalima; 22. Babban Teku (Bahar Maliya)Tambayoyi

 • Wanene matashi da ke wannan hoton, ina yake zama, menene sunan mamarsa da kakarsa?
 • Menene Timothawus ya ce sa’ad da Bulus ya tambaye shi ko zai so ya bi shi da Sila wajen yi wa mutane a wasu ƙasashe wa’azi?
 • Ina ne aka soma kiran mabiyan Yesu Kiristoci?
 • Bayan da Bulus da Barnaba suka bar Antakiya, waɗanne birane ne suka kai ziyara?
 • Ta yaya Timothawus ya taimaki Bulus, wace tambaya ce ya kamata matasa a yau su tambayi kansu?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta A. M. 9:19-30.

  Ta yaya manzo Bulus ya yi amfani da basira sa’ad da ya fuskanci hamayya ga bishara? (A. M. 9:22-25, 29, 30; Mat. 10:16)

 • Ka karanta A. M. 11:19-26.

  Ta yaya labarin da ke A. M. 11:19-21, 26 ya nuna cewa ruhun Jehobah yana yi wa aikin wa’azi ja-gora?

 • Ka karanta Ayukan Manzanni 13:13-16, 42-52.

  Ta yaya A. M. 13:51, 52 ya nuna cewa almajirai ba su ƙyale hamayya ta sa su sanyin gwiwa ba? (Mat. 10:14; A. M. 18:6; 1 Bit. 4:14)

 • Ka karanta A. M. 14:1-6, 19-28.

  Ta yaya furci nan “suka danƙa su ga Ubangiji” yake taimaka wajen sauƙaƙa mu daga alhini da bai dace ba sa’ad da muke taimakon sababbi? (A. M. 14:21-23; 20:32; Yoh. 6:44)

 • Ka karanta A. M. 16:1-5.

  Ta yaya yadda Timothawus ya yi biyayya da yin kaciya ya nanata muhimmancin yin “abu duka sabili da bishara”? (A. M. 16:3; 1 Kor. 9:23; 1 Tas. 2:8)

 • Ka karanta A. M. 18:1-11, 18-22.

  Menene A. M. 18:9, 10 ya nuna game da yadda Yesu ya sa hannu kai tsaye a aikin wa’azi, wane tabbaci ne wannan ya ba mu a yau? (Mat. 28:20)