KA SAN ko waye ne yake kwance a kan hanya? Shawulu ne. Ka tuna cewa shi ne ya kula da babban rigunan mutanen da suka jejjefi Istafanus. Ka dubi hasken nan! Menene yake faruwa?

Bayan an kashe Istafanus, Shawulu ya yi ja-gora wajen neman mabiyan Yesu domin a ji musu. Yana bi gida gida yana kama su yana jefa su kurkuku. Da yawa cikin almajiran suka gudu zuwa wasu birane suna shelar “bishara” a can. Amma Shawulu har wasu birane yake zuwa neman mabiyan Yesu. Yanzu yana kan hanyarsa ce ta zuwa Dimaska. Amma a kan hanyarsa, wani abin mamaki ya faru:

Ba zato sai haske ya haskaka daga sama. Sai ya faɗi ƙasa, kamar yadda kake gani a nan. Sai murya ta ce: ‘Shawulu, Shawulu! Me ya sa kake yi mini rauni?’ Mutanen da suke tare da Shawulu sun ga hasken kuma sun ji muryar amma ba su fahimci abin da ake faɗa ba.

Haske ya makantar da Shawulu

‘Wanene kai, Ubangiji?’ Shawulu ya yi tambaya.

‘Ni ne Yesu wanda kake yi wa rauni,’ in ji muryar. Yesu ya faɗi haka ne domin sa’ad da Shawulu ya yi wa mabiyansa rauni, Yesu yana ji ne kamar shi ake yi wa rauni.

Sai Shawulu ya yi tambaya: ‘To me zan yi, Ubangiji?’

‘Tashi ka shiga cikin Dimasƙa,’ Yesu ya gaya masa. ‘A nan za a gaya maka abin da za ka yi.’ Sa’ad da Shawulu ya tashi ya buɗe idanunsa, ba ya iya ganin kome. Ya makance! Saboda haka mutanen da suke tare da shi suka riƙe hannunsa suka kai shi cikin Dimasƙa.

Sai Yesu ya yi magana da ɗaya cikin almajiransa a Dimaska yana cewa: ‘Ananias ka tashi. Ka tafi titin nan da ake kira Miƙeƙƙe. A gidan Yahuda ka nemi wani mutum mai suna Shawulu. Na zaɓe shi ya zama bawana na musamman.’

Ananias ya yi biyayya. Sa’ad da ya sadu da Shawulu, ya ɗora masa hannu ya ce: ‘Ubangiji ya aike ni domin ka sami gani kuma a cika ka da ruhu mai tsarki.’ A take wani abu mai kama da ɓawo ya faɗi daga idanunsa, kuma ya fara gani.

An yi amfani da Shawulu ƙwarai wajen yi wa mutanen wasu al’ummai wa’azi. Aka san shi da suna manzo Bulus, kuma za mu koyi game da shi. Amma kafin nan bari mu ga abin da Allah ya aiki Bitrus ya yi.

Ayukan Manzanni 8:1-4; 9:1-20; 22:6-16; 26:8-20.Tambayoyi

 • Menene Shawulu ya yi bayan aka kashe Istafanus?
 • Sa’ad da Shawulu yake hanya zuwa Dimaska, wane abin mamaki ne ya faru?
 • Menene Yesu ya gaya wa Shawulu ya yi?
 • Wane umurni ne Yesu ya ba wa Ananias, ta yaya Shawulu ya soma gani kuma?
 • Da wane suna ne aka san Shawulu da shi, kuma yaya aka yi amfani da shi?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Ayukan Manzanni 8:1-4.

  Ta yaya hamayya da ta faɗa wa ikilisiyar Kirista da aka kafa sabo ya sa aka yaɗa bangaskiya ta Kirista, kuma yaya hakan ya faru a wannan zamani? (A. M. 8:4; Isha. 54:17)

 • Ka karanta Ayukan Manzanni 9:1-20.

  Wane irin aiki uku ne Yesu ya bayyana yake son Shawulu ya yi? (A. M. 9:15; 13:5; 26:1; 27:24; Rom. 11:13)

 • Ka karanta Ayukan Manzanni 22:6-16.

  Ta yaya za mu zama kamar Ananias, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci? (A. M. 22:12; 1 Tim. 3:7; 1 Bit. 1:14-16; 2:12)

 • Ka karanta Ayukan Manzanni 26:8-20.

  Ta yaya tuban Shawulu zuwa Kiristanci ya zama abin ƙarfafa ga waɗanda abokan aurensu ba masu bi ba ne? (A. M. 26:11; 1 Tim. 1:14-16; 2 Tim. 4:2; 1 Bit. 3:1-3)