MUTUMIN da ya ɗurkusa a nan Istafanus ne. Almajirin Yesu ne mai aminci. Amma dubi abin da yake faruwa da shi a nan! Waɗannan mutanen suna jifansa da duwatsu. Me ya sa suka ƙi Istafanus haka har suke yi masa irin wannan mugun abu? Bari mu gani.

Ana jejjefe Istifanus

Allah ya taimaki Istafanus ya yi mu’ujizai masu ban mamaki. Waɗannan mutane ba sa son haka, sai suka fara jayayya da shi game da koyar da mutane gaskiya. Amma Allah ya ba wa Istafanus hikima mai yawa, kuma Istafanus ya nuna cewa abin da waɗannan mutane suke koyarwa ba gaskiya ba ne. Wannan ya ba su haushi sosai. Suka kama shi suka kira wasu mutane suka yi masa shaidar zur.

Babban firist ya tambayi Istafanus: ‘Waɗannan koyarwa gaskiya ne?’ Istafanus ya amsa ta wajen ba da jawabi mai kyau daga Littafi Mai Tsarki. A ƙarshe ya nuna yadda miyagun mutane suka ƙi annabawan Jehobah na dā. Sai kuma ya ce: ‘Kuma kuna daidai da waɗannan mutane. Kun kashe bawan Allah Yesu, kuma ba ku yi wa dokokin Allah biyayya ba.’

Wannan ya sa shugabannin addini suka yi fushi ƙwarai! Suka ciji haƙoransu domin haushi. Amma Istafanus ya ɗaga kansa ya ce: ‘Duba! Na ga Yesu yana tsaye a hannun dama na Allah a sama.’ Sai mutanen suka toshe kunnuwansu suka yi maza suka kama Istafanus. Suka kama shi suka ja shi zuwa bayan gari.

A nan suka tuɓe manyan rigunansu suka ba wa saurayi Shawulu ya kula da su. Ka ga Shawulu? Wasu cikin mutanen suka fara jifan Istafanus. Istafanus ya durƙusa, kamar yadda kake gani a nan, ya yi wa Allah addu’a: ‘Jehobah kada ka yi musu horo domin wannan mugunta da suka yi.’ Ya sani cewa wasu cikin shugabannin addini ne suka ruɗe su. Bayan haka Istafanus ya mutu.

Idan wani ya yi maka abin da ba shi da kyau, kana ƙoƙarin ka rama, ko kuma kana roƙon Allah ya ji musu? Ba haka Istafanus ko kuma Yesu suka yi ba. Sun yi wa mutane kirki har da mutanen da ba su yi musu kirki ba. Bari mu yi ƙoƙari mu bi misalinsu.

Ayukan Manzanni 6:8-15; 7:1-60.Tambayoyi

 • Wanene Istafanus, menene Allah yake taimakon shi ya yi?
 • Menene Istafanus ya faɗa da ya sa shugabanan addinai fushi?
 • Sa’ad da mutane suka ja Istafanus zuwa bayan gari, menene suka yi masa?
 • A cikin wannan hoton, wanene saurayin da ke tsaye kusa da tufafi?
 • Kafin ya mutu, menene Istafanus ya yi wa Jehobah addu’a a kai?
 • Ta yin koyi da Istafanus, menene ya kamata mu yi sa’ad da wani ya yi mana laifi?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Ayukan Manzanni 6:8-15.

  Waɗanne ayyukan ruɗu ne shugabanan addinai suka yi amfani da shi don su daina aikin wa’azi na Shaidun Jehobah? (A. M. 6:9, 11, 13)

 • Ka karanta Ayukan Manzanni 7:1-60.

  Menene ya taimaki Istafanus ya ba da amsa da kyau game da bisharar a gaban Majalisa, menene za mu koya daga misalinsa? (A. M. 7:51-53; Rom. 15:4; 2 Tim. 3:14-17; 1 Bit. 3:15)

  Wane hali ne ya kamata mu kasance da shi game da masu hamayya da aikinmu? (A. M. 7:58-60; Mat. 5:44; Luk 23:33, 34)