DUBI mala’ika yana buɗe ƙofar kurkuku. Waɗanda yake ’yantarwa manzannin Yesu ne. Bari mu ga abin da ya sa aka saka su cikin kurkuku.

Mala’ika yana ’yantar da almajiran

Bai daɗewa da aka zubo da ruhu mai tsarki a kan almajiran Yesu ba. Ga abin da ya faru: Wata rana Bitrus da Yohanna suna shiga cikin haikali a Urushalima da rana. A nan a kusa da ƙofa, akwai wani mutumin da gurgu ne tun aka haife shi. Mutane suna kai shi wurin domin ya roƙi kuɗi daga waɗanda suke shiga haikalin. Da ya ga Bitrus da Yohanna, sai ya roƙe su su ba shi wani abu. Menene manzannin za su yi?

Suka tsaya suka dubi mutumin. ‘Ba ni da kuɗi,’ in ji Bitrus, ‘amma zan ba ka abin da nake da shi. Cikin sunan Yesu ka tashi tsaye ka yi tafiya!’ Sai Bitrus ya riƙe hannun mutumin na dama ya ta da shi, sai ya yi tsalle ya fara tafiya. Sa’ad da mutane suka ga wannan, suka yi mamaki suka yi farin ciki domin wannan mu’ujiza mai ban mamaki.

‘Da ikon Allah ne wanda ya ta da Yesu daga matattu muka yi wannan mu’ujiza,’ in ji Bitrus. Sa’ad da shi da Yohanna suke magana, wasu shugabannin addini suka zo. Suka yi fushi domin Bitrus da Yohanna suna gaya wa mutane cewa an tashi Yesu daga matattu. Saboda haka suka kama su suka jefa su kurkuku.

Washegari sai shugabannin addinin suka yi wani babban taro. Suka shigo da Bitrus da Yohanna da kuma mutumin da suka warkar. ‘Da ikon waye kuka yi wannan mu’ujiza?’ shugabannin addinin suka yi tambaya.

Bitrus ya gaya musu cewa da ikon Allah ne, wanda ya ta da Yesu daga matattu. Firistocin ba su san abin da za su yi ba, domin ba za su iya musanta cewa wannan mu’ujiza ta faru ba. Sai suka yi wa manzannin gargaɗi cewa kada su sake yin magana game da Yesu, sai suka ƙyale su.

Da shigewar kwanaki manzannin suka ci gaba da wa’azi game da Yesu suna kuma warkar da marasa lafiya. Labarin wannan mu’ujiza ta yaɗu. Saboda haka jama’a daga garuruwa da suke kusa da Urushalima suka kawo marasa lafiya ga manzannin su warkar da su. Wannan ya sa shugabannin addinin suka yi kishi, suka kama manzannin suka jefa su kurkuku. Amma ba su daɗe ba a ciki.

Daddare mala’ikan Allah ya buɗe ƙofar kurkukun kamar yadda kake gani a nan. Mala’ikan ya ce: ‘Ku tafi ku tsaya a cikin haikali ku yi ta magana da mutane.’ Washegari, sa’ad da shugabannin addinai suka tura mutane kurkukun su kawo manzannin ba sa nan. Daga baya mutane suka same su suna koyarwa a cikin haikali suka kama su suka kai su gaban Majalisa.

‘Mun dokace ku kada ku koyar game da Yesu,’ in ji shugabannin addinan. ‘Amma ga shi kun cika Urushalima da koyarwarku.’ Manzannin suka amsa suka ce: ‘Dole ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutane.’ Sai suka ci gaba da koyar da “bishara.” Wannan misali ne mai kyau da ya kamata mu bi, ko ba haka ba?

Ayukan Manzanni sura 3 zuwa 5.Tambayoyi

 • Menene ya faru da Bitrus da Yohanna wata rana sa’ad da suke zuwa haikali?
 • Menene Bitrus ya ce wa wani gurgu, kuma menene Bitrus ya ba shi da ya fi kuɗi amfani?
 • Me ya sa shugabannan addinai suka yi fushi, menene suka yi wa Bitrus da Yohanna?
 • Menene Bitrus ya gaya wa shugabannan addinai, kuma wane gargaɗi ne manzannin suka karɓa?
 • Me ya sa shugabanan addinai suke kishi, menene ya faru sa’ad da aka saka manzannin cikin kurkuku lokaci na biyu?
 • Ta yaya manzannin suka amsa sa’ad da aka kawo su majami’ar Majalisa?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Ayyukan Manzanni 3:1-10.

  Ko da ba mu da ikon yin mu’ujizai a yau, ta yaya kalmomin Bitrus da ke Ayukan Manzanni 3:6, ya taimake mu mu ga amfanin saƙon Mulkin? (Yoh. 17:3; 2 Kor. 5:18-20; Filib. 3:8)

 • Ka karanta Ayukan Manzanni 4:1-31.

  Sa’ad da muka fuskanci hamayya a hidimarmu, a wace hanya ce ya kamata mu yi koyi da ’yan’uwanmu na ƙarni na farko? (A. M. 4:29, 31; Afis. 6:18-20; 1 Tas. 2:2)

 • Ka karanta Ayukan Manzanni 5:17-42.

  Ta yaya wasu da ba Shaidu ba ne a yanzu da kuma dā suka nuna sanin ya kamata game da aikin wa’azi? (A. M. 5:34-39)