Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Labari na 105: Suna Jira a Urushalima

Labari na 105: Suna Jira a Urushalima

WAƊANNAN mutanen da suke nan mabiyan Yesu ne. Sun yi masa biyayya sun jira a Urushalima. Sa’ad da dukansu suna jira tare, sai ƙara mai ƙarfi ta cika gidan da suke. Ƙarar kamar ta iska ce mai busawa da ƙarfi. Sai harshen wuta ya fara bayyana a kan kowane almajiri. Kana ganin wutar a kan kowannensu? Menene dukan wannan yake nufi?

Ruhu mai tsarki bisa almajirai na ƙarni na farko

Mu’ujiza ce! Yesu ya koma wurin Ubansa a sama, kuma ya zubo da ruhu mai tsarki na Allah a kan mabiyansa. Ka san abin da wannan ruhu mai tsarki ya sa suka yi? Suka fara magana da yare dabam dabam.

Mutane da yawa a Urushalima sun ji ƙarar kamar ta iska mai ƙarfi kuma suka fito su ga abin da yake faruwa. Wasu mutanen daga wasu ƙasashe suke, sun zo domin su yi bikin Isra’ilawa na Fentikos. Waɗannan baƙi sun ga abin mamaki! Suka ji almajiran suna magana da yarensu game da abubuwa masu ban al’ajabi da Allah ya yi.

‘Waɗannan mutanen dukan su daga Galili suke,’ in ji baƙin. ‘To, ta yaya suka koyi waɗannan yare dabam dabam na wasu ƙasashen da muka fito?’

Bitrus ya tashi ya yi musu bayani. Ya ɗaga muryarsa ya gaya wa mutanen game da yadda aka kashe Yesu da kuma cewa Jehobah ya tashe shi daga matattu. ‘Yanzu Yesu yana sama a hannun dama na Allah,’ in ji Bitrus. ‘Kuma ya zubo ruhu mai tsarki. Shi ya sa kuka ji kuma kuka ga wannan mu’ujiza.’

Da Bulus ya faɗi haka, mutane da yawa suka yi baƙin ciki domin abin da aka yi wa Yesu. ‘Menene za mu yi?’ suka yi tambaya. Bitrus ya gaya musu: ‘Kuna bukatar ku canja rayuwarku kuma ku yi baftisma.’ Saboda haka a wannan ranar wajen mutane 3,000 suka yi baftisma suka zama mabiyan Yesu.

Ayukan Manzanni 2:1-47.Tambayoyi

 • Yadda wannan hoton ya nuna, menene ya faru da mabiyan Yesu da suke jira a Urushalima?
 • Wane abin mamaki ne baƙi suka gani a Urushalima?
 • Menene Bitrus ya bayyana wa mutanen?
 • Yaya mutane suka ji bayan sun saurari Bitrus, kuma menene ya gaya musu?
 • Mutane nawa ne suka yi baftisma a ranar Fentakos ta shekara ta 33 A.Z.?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Ayukan Manzanni 2:1-47.

  Ta yaya kalmomin Bitrus da ke Ayukan Manzanni 2:23, 36, ya nuna cewa dukan al’ummar Yahudawa ne suke da alhakin mutuwar Yesu? (1 Tas. 2:14, 15)

  Ta yaya Bitrus ya kafa misali mai kyau a wajen yin mahawara daga Nassosi? (A. M. 2:16, 17, 29, 31, 36, 39; Kol. 4:6)

  Ta yaya Bitrus ya yi amfani da “maƙulai na mulkin sama,” da Yesu ya yi alkawari zai ba shi? (A. M. 2:14, 22-24, 37, 38; Mat. 16:19)