Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 102: Yesu Yana da Rai

Labari na 102: Yesu Yana da Rai

KA SAN ko su wanene waɗannan mutanen biyu da kuma wannan matar? Matar Maryamu Magdaliya ce, abokiyar Yesu. Kuma mutanen da suke sanye da fararen kayan mala’iku ne. Wannan ƙaramin ɗaki da Maryamu take kallo inda aka ajiye gawar Yesu ne bayan ya mutu. Ana kiransa kabari. Amma yanzu babu gawar a ciki! Waye ya ɗauke ta? Bari mu gani.

Mala’iku suna yi wa Maryamu Magdaliya magana

Bayan Yesu ya mutu, firistoci suka ce wa Bilatus: ‘Sa’ad da Yesu yake da rai ya ce za a tashe shi bayan kwana uku. Saboda haka ka ba da umurni a yi gadin kabarin. Saboda haka almajiransa ba za su sace gawar su ce an tashe shi ba daga matattu!’ Bilatus ya gaya wa firistoci su aika da sojoji su tsare kabarin.

Amma da asuba a rana ta ukun bayan Yesu ya mutu farat ɗaya sai mala’ikan Jehobah ya bayana. Ya ture dutsen da aka rufe kabarin da shi. Sojojin suka tsorata ƙwarai har suka kasa motsi. A ƙarshe, sa’ad da suka duba cikin kabarin gawar ba ta nan! Wasu sojojin suka je cikin birni suka gaya wa firistoci. Ka san abin da waɗannan miyagun firistoci suka yi? Suka bai wa sojojin kuɗi su yi ƙarya. Firistocin suka ce wa sojojin su ce: ‘Sa’ad da muna barci da dare almajiransa suka zo suka sace gawarsa.’

Amma a wannan lokacin, wasu mata abokan Yesu suka ziyarci kabarin. Suka yi mamaki da suka ga babu kome a ciki! Farat ɗaya sai mala’iku biyu da fararen kaya suka bayyana. ‘Me ya sa kuke neman Yesu a nan?’ suka yi tambaya. ‘An riga an tashe shi. Ku yi maza ku je ku gaya wa almajiransa.’ Matan suka yi ta gudu! Amma da suke tafiya a kan hanya wani mutum ya tare su. Ka san ko wanene ne? Yesu ne! Ya ce: ‘Ku je ku gaya wa almajirai na.’

Sa’ad da matan suka gaya wa almajiran cewa Yesu yana da rai kuma sun gan shi, almajiran ba su yarda ba. Bitrus da Yohanna suka ruga zuwa kabarin domin su gani da kansu, amma babu kome a cikin kabarin! Sa’ad da Bitrus da Yohanna suka tafi, sun bar Maryamu Magdaliya a nan. Sa’an nan ne ta dubi cikin kabarin ta ga mala’ikun biyu.

Ka san abin da ya faru da jikin Yesu? Allah ya sa ya ɓace. Allah bai tashi Yesu da jikin da ya mutu da shi ba. Allah ya ba Yesu sabon jiki na ruhu, irin wanda mala’ikun da ke sama suke da shi. Amma domin ya nuna wa almajiransa cewa yana da rai, Yesu yana ɗaukan jiki wanda mutane za su iya gani, kamar yadda za mu gani.

Matta 27:62-66; 28:1-15; Luka 24:1-12; Yohanna 20:1-12.Tambayoyi

 • Wacece matar da ke wannan hoton, su wanene maza biyun, ina suke kuma?
 • Me ya sa Bilatus ya gaya wa firistoci su aika sojoji su tsare kabarin Yesu?
 • Menene mala’ika ya yi da sassafe a rana ta uku bayan mutuwar Yesu, amma menene firistocin suka yi?
 • Me ya sa wasu mata suka yi mamaki sa’ad da suka ziyarci kabarin Yesu?
 • Me ya sa Bitrus da Yohanna suka gudu zuwa kabarin Yesu, kuma me suka gani?
 • Menene ya faru da jikin Yesu, menene ya yi don ya nuna wa almajiran cewa yana da rai?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Matta 27:62-66; 28:1-15;

  A lokacin tashin Yesu daga matattu, ta yaya shugaban firistoci, Farisawa da manyan malamai suka yi zunubi ga ruhu mai tsarki? (Mat. 12:24, 31, 32; 28:11-15)

 • Ka karanta Luka 24:1-12.

  Ta yaya labarin tashin Yesu daga matattu ya nuna cewa Jehobah ya ɗauki mata a matsayin tabbatattun shaidu? (Luka 24:4, 9, 10; Mat. 28:1-7)

 • Ka karanta Yohanna 20:1-12.

  Ta yaya Yohanna 20:8, 9 ya taimake mu mu ga bukatar yin haƙuri idan ba mu fahimci cikar annabci na Littafi Mai Tsarki ba? (Mis. 4:18; Mat. 17:22, 23; Luk. 24:5-8; Yoh. 16:12)