BAYAN Bitrus da Yohanna sun bar kabarin da aka ajiye gawar Yesu, sun bar Maryamu a nan ita kaɗai. Sai ta fara kuka. Sai ta dubi cikin kabarin, kamar yadda muka gani a hoto na baya. A nan ta ga mala’iku biyu! Sai suka tambaye ta: ‘Me ya sa kike kuka?’

Maryamu ta amsa: ‘Sun ɗauke Ubangiji na, kuma ban san inda suka ajiye shi ba.’ Da Maryamu ta juya sai ta ga wani mutum. Sai ya tambaye ta: ‘Waye kike nema?’

Maryamu tana tsammanin mutumin da yake kula da lambun ne, kuma wataƙila shi ya ɗauki gawar Yesu. Saboda haka ta ce: ‘Idan kai ka ɗauke shi ka gaya mini inda ka ajiye shi.’ Amma wannan mutumin ainihi Yesu ne. Ya ɗauki jiki da Maryamu ba ta gane shi ba. Amma sa’ad da ya kira sunanta, Maryamu ta fahimci cewa Yesu ne. Ta gudu ta je ta gaya wa almajiran: ‘Na ga Ubangiji!’

Daga baya a wannan ranar, sa’ad da biyu cikin almajiran suke tafiya zuwa ƙauyen Imwasu, wani mutum ya kama tafiya tare da su. Almajiran suna baƙin ciki domin an kashe Yesu. Amma sa’ad da suka ci gaba da tafiya, mutumin ya yi musu bayani game da abubuwa da yawa daga cikin Littafi Mai Tsarki kuma ya sa zuciyarsu ta kwanta. A ƙarshe, da suka tsaya za su ci abinci, almajiran suka gane cewa wannan mutumin Yesu ne. Sai Yesu ya ɓace, sai almajiran biyu suka koma zuwa Urushalima suka gaya wa manzannin game da shi.

Sa’ad da haka yake faruwa, Yesu ya bayyana wa Bitrus. Sauran suka yi farin ciki sa’ad da suka sami wannan labari. Sa’ad da waɗannan almajirai biyu suka isa Urushalima suka sami manzannin, suka gaya musu yadda Yesu ya bayyana musu a kan hanya. Sa’ad da suke gaya musu game da wannan abin, ka san wani abin mamaki da ya faru?

Ka dubi wannan hoton. Yesu ya bayyana a cikin ɗakin ko da yake ƙofar ɗakin a kulle take. Almajiran suka yi farin ciki! Wannan rana ce ta farin ciki. Za ka iya ƙirga ko sau nawa ne Yesu ya bayana ga mabiyansa a yanzu? Ka ƙirga har sau biyar?

Yesu yana bayyana ga almajiran

Manzo Toma ba ya tare da su sa’ad da Yesu ya bayyana. Sai almajiran suka gaya masa: ‘Mun ga Ubangiji!’ Amma Toma ya ce sai ya ga Yesu da kansa kafin ya gaskata. Bayan kwana bakwai almajiran suka kasance tare a cikin ɗaki da yake rufe, kuma a wannan lokaci Toma yana tare da su. Farat ɗaya, Yesu ya bayyana a cikin ɗakin. Sai Toma ya gaskata.

Yohanna 20:11-29; Luka 24:13-43.Tambayoyi

 • Menene Maryamu ta ce wa mutum da take tsammani gadina ne, amma menene ya sa ta fahimci cewa ainihi Yesu ne?
 • Menene ya faru da almajirai biyu da suke tafiya zuwa ƙauyen Imwasu?
 • Wane abin mamaki ne ya faru sa’ad da almajirai biyu suka gaya wa manzannin cewa sun ga Yesu?
 • Sau nawa ne Yesu ya bayana ga manzanninsa?
 • Menene Toma ya ce sa’ad da ya ji cewa almajiran sun ga Ubangiji, amma menene ya faru kwanaki takwas bayan hakan?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Yohanna 20:11-29.

  Yesu yana faɗa a Yohanna 20:23 cewa ’yan adam suna da ikon gafarta zunubai ne? Ka ba da bayani. (Zab. 49:2, 7; Isha. 55:7; 1 Tim. 2:5, 6; 1 Yoh. 2:1, 2)

 • Ka karanta Luka 24:13-43.

  Ta yaya za mu shirya zuciyarmu domin ta karɓi gaskiya ta Littafi Mai Tsarki? (Luk 24:32, 33; Ezra 7:10; Mat. 5:3; A. M. 16:14; Ibran. 5:11-14)