’Yar Jephthah

KA TAƁA yin alkawari kuma daga baya ya yi maka wuya ka cika? Wannan mutumin na hoton nan ya yi haka, kuma abin da ya sa ke nan yake baƙin ciki. Mutumin gwarzon alƙali ne na Isra’ila mai suna Jephthah.

Jephthah ya rayu ne a lokacin da Isra’ilawa ba sa bauta wa Jehobah. Suka sake komawa ga yin miyagun abubuwa. Saboda haka Jehobah ya ƙyale mutanen Ammon su zalunce su. Hakan ya sa Isra’ila suka yi kuka ga Jehobah: ‘Mun yi maka zunubi. Don Allah, ka cece mu!’

Jephthah da mutanensa

Mutanen suka tuba daga miyagun abubuwa da suke yi. Suka nuna cewa sun tuba ta wajen komawa ga bautar Jehobah. Sai Jehobah ya sake taimakonsu.

Mutanen suka zaɓi Jephthah ya yaƙi Ammonawa. Jephthah yana so Jehobah ya taimake shi a yaƙin. Saboda haka ya yi wa Jehobah alkawari: ‘Idan ka ba ni nasara bisa Ammoniyawa, mutumin da ya fito daga gidana da farko ya tare ni sa’ad da na yi nasara zan ba ka shi.’

Jehobah ya saurari alkawarin Jephthah, kuma ya taimake shi ya ci nasara. Sa’ad da Jephthah ya koma gida, ka san waye ya fara zuwa taransa? ’Yarsa ce, tilonsa. ‘Wayyo, ’ya ta!’ in ji Jephthah. ‘Kin jawo mini baƙin ciki. Amma na yi wa Jehobah alkawari, kuma ba zan fasa cika shi ba.’

Sa’ad da ’yar ta fahimci alkawarin da ya yi, da farko ta yi baƙin ciki ƙwarai. Domin wannan yana nufin dole ne ta bar babanta da ƙawayenta. Ta ƙarasa sauran rayuwarta a mazaunin Jehobah a Shiloh. Saboda haka ta gaya wa babanta: ‘Idan ka yi wa Jehobah alkawari, to dole ka cika.’

Saboda haka ’yar Jephthah ta je Shiloh, ta ƙarasa sauran rayuwarta tana bauta wa Jehobah a mazauni. Kwanaki huɗu a kowane shekara ’ya’ya mata na Isra’ila suna zuwa su ziyarce ta a can, suna yin farin ciki tare. Mutanen suka ƙaunaci ’yar Jephthah sosai domin baiwar kirki ce ta Jehobah.

Alƙalawa 10:6-18; 11:1-40.Tambayoyi

 • Wanene Jephthah, kuma wane lokaci ya yi rayuwa?
 • Wane alkawari ne Jephthah ya yi wa Jehobah?
 • Me ya sa Jephthah ya yi baƙin ciki sa’ad da ya dawo gida daga cin nasara bisa Ammonawa?
 • Menene ’yar Jephthah ta ce sa’ad da ta san game da alkawarin babanta?
 • Me ya sa mutanen suke ƙaunar ’yar Jephthah?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Alƙalawa 10:6-18.

  Wane gargaɗi ne daga tarihin Isra’ila na rashin aminci ga Jehobah ya kamata mu bi? (Alƙ. 10:6, 15, 16; Rom. 15:4; R. Yoh. 2:10)

 • Ka karanta Alƙalawa 11:1-11, 29-40.

  Ta yaya muka sani cewa da yake Jephthah ya ba da ’yarsa “hadaya ta ƙonawa” ba ya nufin ya miƙa ta hadaya ta wuta? (Alƙa. 11:31; Lev. 16:24; K. Sha 18:10, 12)

  Ta yaya Jephthah ya miƙa ’yarsa hadaya?

  Menene muka koya daga halin Jephthah game da alkawarinsa ga Jehobah? (Alƙa. 11:35, 39; M. Wa. 5:4, 5; Mat. 16:24)

  Ta yaya ’yar Jephthah ta zama misali mai kyau ga matasa Kiristoci wajen neman hidima ta cikakken lokaci? (Alƙa. 11:36; Mat. 6:33; Filib. 3:8)