Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 51: Ruth da Na’omi

Labari na 51: Ruth da Na’omi

A CIKIN Littafi Mai Tsarki za ka ga wani littafi mai suna Ruth. Tarihin wani iyali ne da suka rayu a lokacin da Isra’ila take da alƙalai. Ruth sunan wata mace ce da ta fito daga ƙasar Mowab; ba ’yar Isra’ila ba ce al’ummar Allah. Amma Ruth ta koyi game da Allah na gaskiya Jehobah, kuma ta ƙaunace shi sosai. Na’omi kuma tsohuwa ce da ta taimaki Ruth ta koyi game da Jehobah.

Na’omi ba’isra’iliya ce. Ita da mijinta da ’yayansu maza biyu suka ƙaura zuwa ƙasar Mowab a lokacin da ake ƙarancin abinci a Isra’ila. Wata rana sai mijin Na’omi ya mutu. Daga baya ’ya’yan Na’omi biyu maza suka auri ’yan matan Mowab masu suna Ruth da Orpah. Amma bayan kamar shekara 10, ’ya’yan Na’omi ma suka mutu. Na’omi da mata biyu suka yi baƙin ciki ƙwarai! Menene Na’omi za ta yi a yanzu?

Wata rana Na’omi ta shirya za ta yi doguwar tafiya zuwa garinsu ta koma ga mutanenta. Ruth da Orpah suna so su zauna tare da ita, saboda haka suka tafi tare da ita. Amma bayan sun yi ɗan tafiya tare, sai Na’omi ta juya ga matan ta ce: ‘Ku koma gida wajen uwayenku.’

Na’omi ta sumbaci matan ta yi ban kwana da su. Sai suka fara kuka, domin suna ƙaunar Na’omi sosai. Suka ce: ‘A’a! Ba za mu koma ga mutanen mu ba.’ Sai Na’omi ta amsa ta ce: ‘Dole sai ku koma ’ya’yana. Zai fi muku a gidajenku.’ Sai Orpah ta koma gida. Amma Ruth ta ƙi komawa.

Na’omi ta juya gare ta ta ce: ‘Orpha ta tafi. Ke ma ki koma gida tare da ita.’ Amma sai Ruth ta amsa ta ce: ‘Kada ki yi ƙoƙari ki sa na ƙyale ki! Bari in bi ki. Dukan inda kika je, ni ma nan zan je, inda kika zauna a nan zan zauna. Mutanen ki za su zama mutane na, kuma Allahnki zai zama Allahna. Inda kika mutu kuma a nan zan mutu, kuma a nan za a binne ni.’ Sa’ad da Ruth ta faɗi haka, Na’omi ba ta yi ƙoƙarin mai da ita gida ba kuma.

A ƙarshe matan biyu suka isa Isra’ila. Nan suka koma da zama. Ba tare da ɓata lokaci ba Ruth ta fara aiki a gona, domin lokacin girbin alkama ya yi. Wani mutum mai suna Bo’az ya ƙyale ta ta yi kalan alkama a gonarsa. Ka san ko wacece mamar Bo’az? Rahab ce ta birnin Jericho.

Wata rana Bo’az ya gaya wa Ruth: ‘Na sami labarinki yadda kika yi wa Na’omi kirki. Na san yadda kika ƙyale mamarki da babanki da ƙasarku kika zo kika zauna tare da mutanen da ba ki sani ba dā. Jehobah ya yi miki albarka!’

Ruth ta amsa: ‘Ka yi mini kirki sosai, maigida. Ka sa na yi farin ciki da wannan maganar mai daɗi da ka gaya mini.’ Bo’az yana ƙaunar Ruth sosai, kuma bai daɗe ba suka yi aure. Wannan ya sa Na’omi ta yi farin ciki ƙwarai! Farin cikin Na’omi ya fi ma yawa sa’ad da Ruth da Bo’az suka haifi ɗansu na fari mai suna Obed. Daga baya Obed ya zama kakan Dauda, wanda za mu koyi game da shi a nan gaba.

Ruth da Na’omi

Littifin Ruth.Tambayoyi

 • Ta yaya ne Na’omi ta soma zama a ƙasar Mowab?
 • Su waye ne Ruth da Orpah?
 • Ta yaya ne Ruth da Orpah suka amsa sa’ad da Na’omi ta gaya musu su koma wurin mutanensu?
 • Wanene Boaz, ta yaya ne ya taimaki Ruth da Na’omi?
 • Menene sunan ɗan Boaz da Ruth, kuma me ya sa ya kamata mu tuna da shi?

Ƙarin tambayoyi

 • .Ka karanta Ruth 1:1-17.

  Wane furci mai kyau na ƙauna ta aminci ne Ruth ta furta? (Ruth 1:16, 17)

  Ta yaya halin Ruth ya nuna halin “waɗansu tumaki” ga shafaffu da ke duniya a yau? (Yoh. 10:16; Zech. 8:23)

 • Ka karanta Ruth 2:1-23.

  Ta yaya ne Ruth ta ba da misali mai kyau ga ’yan mata a yau? (Ruth 2:17, 18; Mis. 23:22; 31:15)

 • Ka karanta Ruth 3:5-13.

  Ta yaya Boaz ya ɗauki yadda Ruth ta yarda ta aure shi maimakon saurayi?

  Menene halin Ruth ya koya mana game da ƙauna ta aminci? (Ruth 3:10; 1 Kor. 13:4, 5)

 • Ka karanta Ruth 4:7-17.

  Ta yaya maza Kiristoci a yau za su zama kamar Boaz? (Ruth 4:9, 10; 1 Tim. 3:1, 12, 13; 5:8)