SA’AD da Isra’ilawa suka shiga masifa, sun yi wa Jehobah kuka. Jehobah ya amsa musu ta wajen ba su shugabannai marasa tsoro. Littafi Mai Tsarki ya kira waɗannan shugabannai alƙalai. Joshua ne alƙali na fari, wasu alƙalai kuma na bayansa sune Othniel, Ehud da Shamgar. Biyu daga cikin mutanen da suka taimaki Isra’ila mata ne masu suna Deborah da Jael.

Deborah tana yi wa Barak magana

Deborah annabiya ce. Jehobah yana ba ta bayani game da abin da zai faru a nan gaba, sai kuma ta gaya wa mutanen abin da Jehobah ya ce. Deborah kuma alƙali ce. Tana zaune a ƙarƙashin wani dabino a can wuri mai tuddai, kuma mutane suna zuwa wurinta domin taimako.

A wannan lokaci Jabin ne sarkin Kan’ana. Yana da karusai 900. Rundunarsa tana da ƙarfi sosai da har aka tilasta wa Isra’ilawa da yawa suka zama bayin Jabin. Sunan shugaban sojojin Jabin shi ne Sisera.

Wata rana Deborah ta aika wa Alƙali Barak saƙo ta ce masa: ‘Jehobah ya ce: “Ka ɗauki mutane 10,000 ka ja-gorance su zuwa Dutsen Tabor. A nan zan kawo maka Sisera. Zan ba ka nasara bisansa da kuma sojojinsa.” ’

Barak ya ce wa Deborah: ‘Zan je idan ke ma za ki tare da ni.’ Deborah ta bi shi, amma ta ce wa Barak: ‘Ba za ka sami yabo ba domin nasarar, domin Jehobah zai ba da Sisera ga hannun mace.’ Kuma abin da ya faru ke nan.

Barak ya hau daga Dutsen Tabor domin ya haɗu da sojojin Sisera. Farat ɗaya Jehobah ya tura ambaliya kuma yawancin sojojin abokan gaba suka mutu. Amma Sisera ya sauka daga kan karusarsa ya gudu.

Barak da Jael da Sisera

Bayan wani ɗan lokaci Sisera ya isa tantin Jael. Ta gayyace shi cikin tantin, ta ba shi madara ya sha. Wannan ya sa ya fara jin barci, ba da daɗewa ba ya fara sheƙa barci. Sai Jael ta ɗauki ƙusa na tanti ta buga shi a kan wannan mugun mutum. Daga baya, sa’ad da Barak ya isa, ta nuna masa gawar Sisera! Ka ga abin da Deborah ta faɗa ya zama gaskiya.

A ƙarshe aka kashe Sarki Jabin ma, Isra’ilawa suka sami kwanciyar hankali na ɗan lokaci

Alƙalawa 2:14-22; 4:1-24; 5:1-31.Tambayoyi

 • Su wanene ne alƙalai, kuma menene sunan wasu cikinsu?
 • Wace gata ce ta musamman Deborah ta samu, kuma menene wannan ya ƙunsa?
 • Sa’ad da Sarki Jabin da shugaban sojojinsa Sisera suka yi wa Isra’ila barazana, wane saƙo ne daga Jehobah Deborah ta sanar wa alƙali Barak, kuma wanene ta ce zai sami yabon?
 • Ta yaya ne Jael ta nuna cewa ita mace ce mai gaba gaɗi?
 • Menene ya faru bayan Sarki Jabin ya mutu?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Alƙalawa 2:14-22.

  Ta yaya ne Isra’ilawa suka jawo wa kansu fushin Jehobah, kuma wane darasi za mu koya daga wannan? (Alƙa. 2:20; Mis. 3:1, 2; Ezek. 18:21-23)

 • Ka karanta Alƙalawa 4:1-24.

  Wane darasi ne game da bangaskiya da kuma gaba gaɗi mata Kiristoci za su koya daga misalin Deborah da Jael? (Alƙa. 4:4, 8, 9, 14, 21, 22; Mis. 31:30; 1 Kor. 16:13)

 • Ka karanta Alƙalawa 5:1-31.

  Ta yaya za a iya amfani da waƙar nasara ta Barak da Deborah a addu’a game da yaƙin Har-Magedon mai zuwa? (Alƙa. 5:3, 31; 1 Laba. 16:8-10; R. Yoh. 7:9, 10; 16:16; 19:19-21)