Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 43: Joshua Ya Zama Shugaba

Labari na 43: Joshua Ya Zama Shugaba

MUSA yana so ya shiga ƙasar Kan’ana tare da Isra’ilawa. Saboda haka ya yi roƙo: ‘Ka bari mana in haye Kogin Urdun, Jehobah, domin in ɗan ga albarkar ƙasar.’ Amma Jehobah ya ce: ‘Ya ishe ka haka! Akul ka sake wannan maganar!’ Ka san abin da ya sa Jehobah ya faɗi haka?

Domin abin da ya faru ne sa’ad da Musa ya bugi dutse. Ka tuna, shi da Haruna ba su daraja Jehobah ba. Ba su gaya wa mutanen ba cewa Jehobah ne ya ba su ruwa daga dutsen. Domin wannan Jehobah ya ce ba zai ƙyale su su shiga ƙasar Kan’ana ba.

’Yan watanni bayan Haruna ya mutu, Jehobah ya gaya wa Musa: ‘Ka ɗauki Joshua, ka tsayar da shi a gaban Eleazar firist da kuma mutanen. Kuma a gaban su duka, ka gaya musu duka cewa Joshua ne sabon shugaba.’ Musa ya yi kamar yadda Jehobah ya ce, kamar yadda kake gani a wannan hoton.

Musa yana gabatar da Joshua a matsayin shugaba

Sai kuma Jehobah ya gaya wa Joshua: ‘Ka ƙarfafa, kada ka ji tsoro. Za ka ja-goranci Isra’ilawa zuwa ƙasar Kan’ana da na yi musu alkawari, kuma zan kasance tare da kai.’

Daga baya Jehobah ya gaya wa Musa ya hau can saman Dutsen Nebo a ƙasar Mowab. Daga nan Musa zai iya ganin ketaren Kogin Urdun kuma ya ga kyakkyawar ƙasar Kan’ana. Jehobah ya ce: ‘Wannan ita ce ƙasar da na yi alkawari zan bai wa ’ya’yan Ibrahim, da Ishaku da Yakubu. Na ƙyale ka ka gani, amma ba zan ƙyale ka ka shiga ba.’

A can kan Dutsen Nebo Musa ya mutu. Yana da shekara 120. Har ila yana da ƙarfi, kuma idanunsa ba su dushe ba. Mutane suka yi baƙin ciki suka yi ta kuka domin Musa ya mutu. Amma sun yi farin ciki da Joshua ne ya zama sabon shugabansu.

Litafin Lissafi 27:12-23; Kubawar Shari’a 3:23-29; 31:1-8, 14-23; 32:45-52; 34:1-12.Tambayoyi

 • A wannan hoton waɗanne mutane ne suke tsaye tare da Musa?
 • Menene Jehobah ya gaya wa Joshua?
 • Me ya sa Musa ya hau kan Dutsen Nebo, kuma menene Jehobah ya gaya masa?
 • Musa yana da shekaru nawa ne lokacin da ya mutu?
 • Me ya sa mutanen baƙin ciki, amma wane dalili ne suke da shi na yin farin ciki?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Litafin Lissafi 27:12-23.

  Wane babban aiki ne Jehobah ya ba wa Joshua, kuma ta yaya ne yadda Jehobah yake kula da mutanensa ya bayyana a yau? (Lit. Lis. 27:15-19; A. M. 20:28; Ibran. 13:7)

 • Ka karanta Kubawar Shari’a 3:23-29.

  Me ya sa Jehobah bai ƙyale Musa da Haruna su ƙetare zuwa ƙasar alkawari ba, kuma wane darasi za mu koya daga wannan? (K. Sha 3:25-27; Lit. Lis. 20:12, 13)

 • Ka karanta Kubawar Shari’a 31:1-8, 14-23.

  Ta yaya kalaman ƙarshe na Musa zuwa ga Isra’ila ya nuna cewa ya karɓi horo daga Jehobah? (K. Sha 31:6-8, 23)

 • Ka karanta Kubawar Shari’a 32:45-52.

  Ta yaya ne Kalmar Allah ya kamata ya taɓa rayuwarmu? (K. Sha 32:47; Lev. 18:5; Ibran. 4:12)

 • Ka karanta Kubawar Shari’a 34:1-12.

  Ko da yake Musa bai ta ba gani Jehobah a zahiri ba, menene Kubawar Shari’a 34:10 ta nuna game da dangantakarsa da Jehobah? (Fit. 33:11, 20; Lit. Lis. 12:8)