Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Labari na 42: Jaka Ta Yi Magana

Labari na 42: Jaka Ta Yi Magana

KA TAƁA jin cewa jaka ta yi magana? ‘Wataƙila ka ce, a’a.’ ‘Dabbobi ba sa magana.’ Amma Littafi Mai Tsarki ya faɗi game da jaka da ta yi magana. Bari mu ga yadda ya faru.

Mala’ika

Isra’ilawa suna shirye su shiga cikin ƙasar Kan’ana. Balak, sarkin Mowab, yana tsoron Isra’ilawa. Saboda haka ya aika wani mutum mai wayo mai suna Balaam ya la’anci Isra’ilawa. Balak ya yi alkawarin cewa zai ba wa Balaam kuɗi mai yawa, saboda haka Balaam ya hau jakarsa ya je wajen Balak.

Jehobah ba ya son Balaam ya la’anci mutanensa. Saboda haka ya aiki wani mala’ika da dogon takobi ya tare hanyar Balaam. Balaam bai gan mala’ikan ba, amma jakarsa ta gani. Saboda haka jakar ta yi ta ƙoƙarin ta guje wa mala’ikan, kuma a ƙarshe sai ta kwanta kawai a kan hanyar. Balaam ya yi fushi ƙwarai, ya riƙa dūkan jakar da sanda.

Sai Jehobah ya sa Balaam ya ji jakar tana yi masa magana. ‘Me na yi maka da kake bugu na haka?’ jakar ta yi tambaya.

Balaam a kan jaka

’Kin mai da ni kamar wawa,’ in ji Balaam. ‘Da ina da takobi da na kashe ki!’

‘Na taɓa yi maka haka a dā?’ jakar ta yi tambaya.

‘A’a,’ Balaam ya amsa.

Sai Jehobah ya buɗe idon Balaam ya ga mala’ika da takobi da yake tsaye a kan hanya. Mala’ikan ya ce: ‘Me ya sa ka bugi jakarka? Na zo ne in tare maka hanya, domin kada ka je ka la’anci Isra’ila. Idan ba domin jakarka ta guje ni ba, da na kashe ka, da kuma ban taɓa jakar ba.’

Balaam ya ce: ‘Na yi zunubi. Ban san kana tsaye a kan hanya ba.’ Mala’ikan ya ƙyale Balaam ya tafi, Balaam ya tafi wajen Balak. Duk da haka ya yi ƙoƙari ya la’anci Isra’ila, maimakon haka, Jehobah ya sa ya albarkaci Isra’ila sau uku.

Litafin Lissafi 21:21-35; 22:1-40; 23:1-30; 24:1-25.Tambayoyi

 • Wannene Balak kuma me ya sa ya aika a kira Balaam?
 • Me ya sa jakar Balaam ta kwanta a kan hanya?
 • Menene Balaam ya ji jakar ta ce?
 • Menene mala’ika ya gaya wa Balaam?
 • Menene ya faru sa’ad da Balaam ya yi ƙoƙarin ya la’anci Isra’ila?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta 21:21-35.

  Me ya sa Isra’ila suka yi nasara bisa Sarki Sihon na Amoriyawa da kuma Sarki Og na Bashan? (Lit. Lis. 21:21, 23, 33, 34)

 • Ka karanta Litafin Lissafi 22: 1-40.

  Me ya sa Balaam yake so ya la’anci Isra’ilawa, kuma waɗanne darussa za mu koya daga wannan? (Lit. Lis. 22:16, 17; Mis. 6:16, 18; 2 Bit. 2:15; Yahu. 11)

 • Ka karanta Litafin Lissafi 23:1-30.

  Ko da yake Balaam ya yi magana kamar shi mai bauta wa Jehobah ne, ta yaya ayyukansu suka nuna ba ya bauta wa Jehobah? (Lit. Lis. 23:3, 11-14; 1 Sam. 15:22)

 • Ka karanta Litafin Lissafi 24:1-25.

  Ta yaya wannan tarihin Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa bangaskiyarmu game da cika nufin Jehobah? (Lit. Lis. 24:10; Isha. 54:17)