Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 40: Musa Ya Bugi Dutsen

Labari na 40: Musa Ya Bugi Dutsen

SHEKARU suka yi ta shigewa, shekara 10, shekara 20, shekara 30, har shekara 39! Amma har yanzu Isra’ilawa suna cikin daji. Amma a dukan waɗannan shekaru Jehobah ya kula da mutanensa. Ya ciyar da su da manna. Yana yi musu ja-gora da umudin gajimare da rana da kuma umudin wuta daddare. Kuma a cikin dukan waɗannan shekaru tufafinsu ba su mutu ba kuma ƙafafunsu ba su yi miki ba.

Yanzu ana wata na fari na shekara 40 tun da suka bar ƙasar Masar. Isra’ila suka sake yin zango a Kadesh. A wannan wurin suke sa’ad da aka aiki masu leƙen asiri 12 su leƙi asirin ƙasar Kan’ana kusan shekara 40 da suka shige. Yar Musa Maryamu ta mutu a Kadesh. Kuma kamar dā, da matsala a nan.

Mutanen ba su sami ruwan sha ba. Saboda haka suka fara yi wa Musa mita: ‘Gwamma da mun mutu. Menene ya sa kuka fitar da mu daga Masar kuka kawo mu cikin wannan muguwar wuri inda ba abin da ke tsirowa? Babu hatsi, babu ɓaure ko ruwan anab ko rumana. Babu ma ruwan sha.’

Musa yana bugun dutsen

Sa’ad da Musa da Haruna suka je mazauni su yi addu’a, Jehobah ya gaya wa Musa: ‘Ka tara jama’ar a wuri ɗaya. Sai ka yi magana da wancan dutse a gaban dukansu. Isashen ruwa za ya fito daga cikin sa da zai ishe dukan mutane da dabbobinsu.’

Saboda haka Musa ya tara jama’ar, ya ce: ‘Ku saurara, ku waɗanda ba ku dogara ga Allah ba! Wato, sai ni da Haruna mun samo maku ruwa daga cikin wannan dutsen?’ Sai Musa ya bugi dutsen sau biyu da sandarsa, sai ruwa ya fara kwararowa daga dutsen. Ruwan ya ishe mutane da dabbobinsu sha.

Amma Jehobah ya yi fushi da Musa da Haruna. Ka san abin da ya sa? Domin Musa da Haruna sun ce su ne za su fito da ruwa daga dutse. Amma ainihi Jehobah ne ya fito da shi. Kuma domin Musa da Haruna ba su faɗi gaskiya game da wannan ba, Jehobah zai yi musu horo. ‘Ba za ku ja-goranci mutanen zuwa ƙasar Kan’ana ba,’ Jehobah ya ce.

Ba da daɗewa ba Isra’ilawa suka tashi daga Kadesh. Bayan ɗan lokaci suka isa Dutsen Hor. A nan a kan dutsen, Haruna ya mutu. Yana da shekara 123 a lokacin da ya mutu. Isra’ilawa suka yi baƙin ciki sosai, saboda haka suka yi kwana 30 suna yin makoki ga Haruna. Ɗansa Eleazar ya zama babban firist na al’ummar Isra’ila.

Litafin Lissafi 20:1-13, 22-29; Kubawar Shari’a 29:5.Tambayoyi

 • Ta yaya Jehobah ne ya kula da Isra’ilawa sa’ad da suke cikin daji?
 • Wace mita ce Isra’ila suka yi sa’ad da suka yi zango a Kedesh?
 • Ta yaya ne Jehobah ya yi tanadin ruwa ga mutanen da kuma dabbobinsu?
 • A wannan hoto wanene ne yake nuna kansa, kuma me ya sa ya yi haka?
 • Me ya sa Jehobah ya yi fushi da Musa da Haruna, kuma ta yaya aka yi musu horo?
 • Me ya faru a Dutsen Hor, kuma wanene ya zama babban firist na Isra’ila?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Litafin Lissafi 20:1-13, 22-29 da kuma Kubawar Shari’a 29:5.

  Menene muka koya daga yadda Jehobah ya kula da Isra’ilawa a daji? (K. Sha 29:5; Mat. 6:31; Ibran. 13:5; Yaƙ. 1:17)

  Yaya Jehobah ya ɗauki kasawar Musa da Haruna su ɗaukaka shi a gaban Isra’ilawa? (Lit. Lis. 20:12; 1 Kor. 10:12; R. Yoh. 4:11)

  Me za mu koya daga yadda Musa ya karɓi horo daga Jehobah? (Lit. Lis. 12:3; 20:12, 27, 28; K. Sha 32:4; Ibran. 12:7-11)