KA SAN ko menene wannan ginin? Tanti ne na musamman domin bautar Jehobah. Ana kuma kiransa mazauni. Mutanen sun kammala gina shi shekara ɗaya bayan sun fita daga ƙasar Masar. Ka san ko ra’ayin wanene ne su gina shi?

Mazauni

Ra’ayin Jehobah ne. Sa’ad da Musa yake kan Dutsen Sinai, Jehobah ya gaya masa yadda zai gina shi. Ya gaya masa ya gina shi domin ya kasance da sauƙin warwarewa. A haka za a iya ɗaukansa zuwa wani wuri dabam, a sake harhaɗawa. Saboda haka duk inda Isra’ilawa suka yi zango a cikin daji, za su tafi da shi.

Idan ga dubi cikin ɗan ɗaki da ke ƙarshen tantin za ka ga akwati. Ana kiran wannan akwatin alkawari. Yana da mala’iku biyu da aka yi da zinariya, a kowane ɓangare. Allah ya sake rubuta Dokokin Goma a kan wasu alluna biyu domin Musa ya fasa na farkon. Kuma waɗannan duwatsun suna cikin sunduƙin alkawarin. Da kuma tukunya da manna a cikinta. Ka tuna ko menene manna?

Haruna yayan Musa ne Jehobah ya zaɓa ya zama babban firist. Ya shugabanci mutanen wajen bauta wa Jehobah. Kuma ’ya’yansa ma suka zama firistoci.

Yanzu dubi babban ɗakin tantin. Ya yi biyun ƙaramin ɗakin. Ka ga akwati da hayaki yake tashi daga cikinsa? Wannan bagadi ne inda firist yake ƙona abubuwa masu ƙamshi da ake kira turaren hayaƙi. Akwai kuma fitila mai rassa bakwai. Abu na uku kuma da ke cikin ɗakin teburi ne. Ana ajiye burodi 12 a kai.

A cikin filin mazaunin kuma da akwai babbar tasa da take cike da ruwa. Firistoci suna amfani da shi domin wanki. Da akwai kuma babban bagadi. A nan ake ƙona dabbobin da aka yanka domin hadaya ga Jehobah. Tantin yana tsakiyar inda Isra’ilawa suka yi zango.

Fitowa 25:8-40; 26:1-37; 27:1-8; 28:1; 30:1-10, 17-21; 34:1, 2; Ibraniyawa 9:1-5.Tambayoyi

 • Menene ake kiran ginin da ke hoton nan, kuma menene aike yi a ciki?
 • Me ya sa Jehobah ya gaya wa Musa ya yi wannan tanti domin a naɗe shi da sauƙi?
 • Wanene wannan akwati da ke ƙaramin ɗaki a ƙarshen tantin, kuma menene yake cikin akwatin?
 • Wanene Jehobah ya zaɓa ya zama babban firist, kuma menene aikin babban firist ɗin?
 • Ka faɗi abubuwa uku da suke cikin babban ɗakin tantin.
 • Waɗanne abubuwa biyu ne suke filin mazaunin, kuma me ake yi da su?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Fitowa 25:8-40; 26:1-37; 27:1-8; da kuma 28:1.

  Menene mala’ikun da suke ‘kan akwatin’ suke wakilta? (Fit. 25:20, 22; Lit. Lis. 7:89; 2 Sar. 19:15)

 • Ka karanta Fitowa 30:1-10, 17-21; 34:1, 2; da kuma Ibraniyawa 9:1-5.

  Me ya sa Jehobah ya nanata muhimmanci tsabta ta jiki ga firistocin da suke hidima a mazauni, kuma ta yaya wannan zai shafe mu a yau? (Fit. 30:18-21; 40:30, 31; Ibran. 10:22)

  Ta yaya manzo Bulus ya nuna cewa mazauni da Dokar alkawari sun shuɗe a lokacin da yake rubuta wasiƙarsa zuwa ga Kiristoci Ibraniyawa? (Ibran. 9: 1, 9; 10: 1)