Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 49: Rana Ta Tsaya Wuri Ɗaya

Labari na 49: Rana Ta Tsaya Wuri Ɗaya

DUBI Joshua. Yana cewa: ‘Rana, tsaya wuri ɗaya!’ Kuma rana ta tsaya wuri ɗaya. Ta tsaya daidai tsakar rana har yini guda. Jehobah ya sa ya faru! Amma bari mu ga abin da ya sa Joshua yake so rana ta ci gaba da haskakawa.

Rana

Sa’ad da miyagun sarakuna biyar na ƙasar Kan’ana suka fara yaƙi da Gibeyonawa, Gibeyonawan suka aiki wani mutum ya nemi taimako wajen Joshua. ‘Ku zo wurinmu da sauri!’ in ji shi. ‘Ku cece mu! Dukan sarakuna da suke kan tuddai sun zo su yaƙi bayinku.’

Nan da nan Joshua da mayaƙansa suka tafi. Sun yi tafiya dukan dare. Da suka isa Gibeyon sojojin dukan sarakuna biyar suka tsorata suka fara gudu. Sai Jehobah ya zubo da manyan ƙanƙara daga sama, ƙanƙarar ta kashe sojoji fiye da waɗanda mayaƙan Joshua suka kashe.

Joshua

Joshua ya lura cewa ba da daɗewa ba rana za ta faɗi. Dare zai yi, kuma sojojin miyagun sarakuna biyar ɗin za su gudu. Abin da ya sa ke nan Joshua ya yi wa Jehobah addu’a kuma ya ce: ‘Rana, tsaya wuri ɗaya!’ Da rana ta ci gaba da haskakawa, Isra’ilawan suka kammala cin nasara a yaƙin.

Da akwai miyagun sarakuna da yawa a ƙasar Kan’ana da ba sa son mutanen Allah. Ya ɗauki Joshua da sojojinsa wajen shekara shida kafin su kammala cin sarakuna 31 a yaƙi. Bayan da suka gama wannan, Joshua ya tabbata an raba waɗannan ƙasa ga ƙabilu da har yanzu suna bukatar yanki.

Shekaru da yawa suka shige, Joshua ya mutu a ƙarshe yana da shekara 110. Sa’ad da shi da abokansa suke da rai, mutane suna yi wa Jehobah biyayya. Amma sa’ad da waɗannan mutanen kirki suka mutu, mutanen suka fara yin miyagun abubuwa kuma suna shiga cikin masifa. Wannan lokaci ne da suke bukatar taimakon Allah sosai.

Joshua 10:6-15; 12:7-24; 14:1-5; Alƙalawa 2:8-13.Tambayoyi

 • A wannan hoto menene Joshua yake faɗa, kuma me ya sa?
 • Ta yaya ne Jehobah ya taimaki Joshua da mayaƙansa?
 • Sarakuna nawa ne Joshua ya ci nasara a kansu kuma yaya tsawon lokacin?
 • Me ya sa Joshua ya raba ƙasar Kan’ana?
 • Shekarar Joshua nawa ne sa’ad da ya mutu, kuma menene ya faru da mutanen bayan haka?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Joshua 10:6-15.

  Sanin Jehobah ya sa rana da wata su tsaya wuri ɗaya domin Isra’ila, ya ba mu wane tabbaci ne yau? (Josh. 10:8, 10, 12, 13; Zab. 18:3; Mis. 18:10)

 • Ka karanta Joshua 12:7-24.

  Wanene ainihi ya yi nasara a kan sarakuna 31 na Kan’ana, kuma me ya sa wannan yake da muhimmanci a gare mu a yau? (Josh. 12:7; 24:11-13; K. Sha 31:8; Luk 21:9, 25-28)

 • Ka karanta Joshua 14:1-5.

  Ta yaya aka raba ƙasar a tsakanin ƙabilun Isra’ila, kuma menene wannan ya nuna game da gado a Aljanna? (Josh. 14:2; Isha. 65:21; Ezek. 47:21-23; 1 Kor. 14:33)

 • Ka karanta Joshua 2:8-13.

  Kamar Joshua a Isra’ila, waye a yau ya kasance mai kāriya daga ridda? (Alƙa. 2:8, 10, 11; Mat. 24:45-47; 2 Tas. 2:3-6; Tit. 1:7-9; R. Yoh. 1:1; 2:1, 2)