Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 47: Ɓarawo a Isra’ila

Labari na 47: Ɓarawo a Isra’ila
Achan yana ɓoye abubuwan da ya sace

DUBI abin da wannan mutumin yake binnewa a cikin tantinsa! Taguwa mai kyau, sandar zinariya da kuma wasu azurfa. Ya kwaso su ne daga birnin Jericho. Amma me ya kamata a yi da abubuwan Jericho? Ka tuna?

Da za a halaka su ne, zinariya da kuma azurfa a zuba su cikin asusun mazaunin Jehobah. Saboda haka waɗannan mutanen sun yi wa Allah rashin biyayya. Sun saci abin Allah. Sunan mutumin Achan ne, kuma waɗanda suke tare da shi iyalinsa ne. Bari mu ga abin da ya faru.

Bayan Achan ya saci waɗannan abubuwa, Joshua ya aiki mutane su yaƙi birnin A’i. Amma sai aka yi nasara a kan su a yaƙin. Aka kashe wasunsu, sauran kuma suka gudu. Joshua ya yi baƙin ciki ƙwarai. Ya kwanta ya yi rub-da-ciki ya yi wa Jehobah addu’a: ‘Me ya sa ka ƙyale wannan ya faru da mu?’

Jehobah ya amsa: ‘Ka tashi! Isra’ila ta yi zunubi. Sun ɗauki wasu abubuwan da ya kamata a halaka ko kuma waɗanda za a bai wa mazaunin Jehobah. Sun saci taguwa mai kyau sun ɓoye. Ba zan albarkace ku ba har sai kun halaka shi.’ Jehobah ya ce zai nuna wa Joshua mugun mutumin da ya yi haka.

Saboda haka Joshua ya tattara duka mutanen, kuma Jehobah ya fito da mugun mutumin Achan. Achan ya ce: ‘Na yi zunubi. Na ga taguwa mai kyau, da kuma sandar zinariya da kuma wasu azurfa. Kuma ina son su sosai saboda haka na ɗauke su. Za ku same su cikin ramin da na binne su a cikin tanti na.’

Sa’ad da suka sami waɗannan abubuwa suka kawo wa Joshua, ya ce wa Achan: ‘Me ya sa ka jawo mana masifa? Yanzu Jehobah zai jawo maka masifa!’ Sai dukan mutanen suka jefi Achan da iyalinsa suka kashe su. Wannan bai nuna mana ba cewa bai kamata ba mu ɗauki abin da ba na mu ba?

Bayan haka Isra’ila ta tafi ta yi yaƙi kuma da A’i. A wannan lokaci Jehobah ya taimaki mutanensa, kuma suka yi nasara a yaƙin.

Joshua 7:1-26; 8:1-29.Tambayoyi

 • A wannan hoton wanene wannan mutumin da yake binne dukiya da ya kwasa daga Jericho, kuma su waye suke taimakonsa?
 • Me ya sa abin da Achan da iyalinsa suka yi ya tsanani sosia?
 • Menene Jehobah ya ce sa’ad da Joshua ya tambayi abin da ya sa aka ci Isra’ilawa a yaƙi da A’i?
 • Bayan an kawo Achan da iyalinsa zuwa wurin Joshua, menene ya same su?
 • Wane darasi mai muhimmanci ne hukuncin Achan ya koya mana?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Joshua 7:1-26.

  Menene addu’ar Joshua ta nuna game da dangantakarsa da Mahaliccinsa? (Josh. 7:7-9; Zab. 119:145; 1 Yoh. 5:14)

  Menene misalin Achan ya nuna, kuma ta yaya wannan ya kasance gargaɗi a garemu? (Josh. 7:11, 14, 15; Mis. 15:3; 1 Tim. 5:24; Ibran. 4:13)

 • Ka karanta 8:1-29.

  Wane hakki ne muke da shi ga ikilisiyar Kirista a yau? (Josh. 7:13; Lev. 5:1; Mis. 28:13)