DUBI! Isra’ilawa suna ƙetare Kogin Urdun! Amma ina ruwan kogin? Domin ana ruwan sama sosai a wannan lokaci na shekara, kogin ya cika sosai ’yan mintoci da suka wuce. Amma yanzu ruwan ya bushe! Kuma Isra’ila suna ƙetarewa a kan busashiyar ƙasar kamar yadda suka yi a Jar Teku! Ina ruwan suka je? Bari mu gani.

Isra’ilawa suna ƙatare Kogin Urdun

Sa’ad da lokaci ya yi domin Isra’ilawa su ƙetare Kogin Urdun, Jehobah ya ce wa Joshua ya gaya wa mutanen cewa: ‘Firistoci su ɗauki akwatin alkawari su shige gaban mutanen. Sa’ad da suka saka ƙafafunsu cikin ruwan Kogin Urdun, ruwan zai daina gudu.’

Saboda haka firistoci suka ɗauki akwatin alkawarin, suka shiga gaban mutanen. Sa’ad da suka isa Urdun, firistoci suka shiga cikin ruwan. Yana gudu sosai kuma da ƙarfi. Amma da zarar ƙafafunsu sun taɓa ruwan, sai ruwan ya fara daina gudu! Mu’ujiza ce! A can sama Jehobah ya tare ruwan. Ba da daɗewa ba babu ruwa kuma a kogin!

Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin suka shiga har tsakiyar kogin da ya bushe. Kana ganinsu a wannan hoton? Suka tsaya a nan har dukan Isra’ilawa suka ƙetare Kogin Urdun a kan busasshiyar ƙasa!

Sa’ad da kowa ya ƙetare, Jehobah ya gaya wa Joshua ya gaya wa mutane masu ƙarfi 12: ‘Su je cikin kogin inda firistoci suke tsaye da akwatin alkawari. Su kwashi duwatsu 12, su tara su a inda za su yi zango daddare. Sa’an nan, a nan gaba, sa’ad da ’ya’yanku suka yi tambaya menene ma’anar waɗannan duwatsu, sai ku gaya musu cewa ruwan ya daina gudu sa’ad da akwatin alkawari na Jehobah ya ƙetare Urdun. Duwatsun za su tuna muku da wannan mu’ujiza!’ Joshua kuma ya tara duwatsu 12 a inda firistocin suka tsaya a cikin kogin.

Joshua

A ƙarshe Joshua ya gaya wa firistoci da suke ɗauke da akwatin alkawarin: ‘Ku fita daga cikin Urdun.’ Suna fita ke nan, kogin ya fara gudu kuma.

Joshua 3:1-17; 4:1-18.Tambayoyi

 • Wace mu’ujiza ce Jehobah ya yi domin Isra’ilawa su ƙetare Kogin Urdun?
 • Wane aikin bangaskiya ne dole Isra’ilawa su yi domin su ƙetare Kogin Urdun?
 • Me ya sa Jehobah ya gaya wa Joshua ya tara manyan duwatsu 12 daga gefen kogin?
 • Menene ya faru da firistoci suka fita daga cikin Kogin Urdun ɗin?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Joshua 3:1-17.

  Kamar yadda wannan labarin ya nuna menene muke bukatar mu yi dominmu sami taimako da kuma albarka daga Jehobah? (Josh. 3:13, 15; Mis. 3:5; Yaƙ. 2:22, 26)

  Yaya ne yanayin Kogin Urdun sa’ad da Isra’ilawa suka ƙetare zuwa Ƙasar Alkawari, kuma ta yaya wannan ya ɗaukaka sunan Jehobah? (Josh. 3:15; 4:18; Zab. 66:5-7)

 • Ka karanta Joshua 4:1-18.

  Menene manufar duwatsu 12 da aka kwasa daga Urdun kuma aka jera a Gilgal? (Josh. 4:4-7)