Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 44: Rahab Ta Ɓoye ’Yan Leƙen Asiri

Labari na 44: Rahab Ta Ɓoye ’Yan Leƙen Asiri

WAƊANNAN mutanen suna cikin matsala. Dole ne su gudu, in ba haka ba za a kashe su. ’Yan leƙen asiri daga Isra’ila ne, kuma sunan matar da take taimaka musu Rahab. Rahab tana da zama cikin wannan gida da yake jikin ganuwar Jericho. Bari mu ga abin da ya sa waɗannan mutanen suke cikin wahala

Isra’ilawa suna shirye su ketare Kogin Urdun su shiga cikin ƙasar Kan’ana. Amma kafin su shiga, Joshua ya aiki ’yan leƙen asiri biyu. Ya gaya musu: ‘Ku je ku dubo ƙasar da kuma birnin Jericho.’

Rahab da Isra’ilawa masu leƙen asiri guda biyu

Sa’ad da ’yan leƙen asirin suka shiga cikin Jericho, sai suka je gidan Rahab. Amma wani ya gaya wa sarkin Jericho: ‘Isra’ilawa biyu sun shigo nan da dare domin su leƙi asirin ƙasar.’ Da ya ji haka, sarkin ya aiki mutane zuwa wurin Rahab, kuma suka umurce ta: ‘Mutanen nan da suke cikin gidanki ki fito da su!’ Amma Rahab ta ɓoye mutanen a cikin rufin gidanta. Sai ta ce: ‘Wasu mutane sun zo gida na, amma ban san daga inda suka fito ba. Sun tafi da yake dare ya fara yi, kafin a rufe ƙofar garin. Idan kun yi sauri, za ku kama su!’ Saboda haka sai mutanen suka fita nemansu.

Bayan sun tafi, Rahab ta yi sauri zuwa rufin gidanta. ‘Na sani Jehobah zai ba ku wannan ƙasar,’ ta gaya wa ’yan leƙen asirin. ‘Mun ji yadda ya busar da Jar Teku sa’ad da ku ka bar ƙasar Masar, da kuma yadda ku ka kashe sarakunan Sihon da na Og. Na yi muku alheri, saboda haka ku yi mini alkawari, don Allah, cewa ku ma za ku yi mini alheri. Ku ceci babana da mamata da ’yan’uwana maza da mata.’

’Yan leƙen asirin suka ce za su yi haka, amma dole ne Rahab ta yi wani abu. ‘Ki karɓi wannan jan igiyar ki ɗaure ta a tagarki,’ in ji ’yan leƙen asirin, ‘kuma ki tara dukan ’yan’uwanki a cikin wannan gida tare da ke. Saboda sa’ad da muka komo mu ci Jericho, za mu ga wannan igiyar a tagarki kuma ba za mu kashe kowa ba a wannan gida.’ Sa’ad da ’yan leƙen asirin suka koma wurin Joshuwa, sun gaya masa dukan abin da ya faru.

Joshua 2:1-24; Ibraniyawa 11:31.Tambayoyi

 • A ina ne Rahab take da zama?
 • Su waye ne waɗannan mutane da suke wannan hoton, kuma me ya kawo su Jericho?
 • Menene sarkin Jericho ya umurci Rahab ta yi, kuma yaya ta amsa?
 • Ta yaya Rahab ya taimaki mutanen biyu, kuma wane tagomashi ne ta nema?
 • Wane alkawari ne ’yan leƙen asiri suka yi wa Rahab?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Joshua 2:1-24.

  Ta yaya ne alkawarin Jehobah da ke rubuce a Fitowa 23:28 ya cika sa’ad da Isra’ilawa suka kai wa Jericho hari? (Josh. 2:9-11)

 • Ka karanta Ibraniyawa 11:31.

  Ta yaya ne misalin Rahab ya nanata muhimmancin bangaskiya? (Rom. 1:17; Ibran. 10:39; Yaƙ. 2:25)