Musa ya shugabanci Isra’ilawa wajen fita daga bauta a ƙasar Masar zuwa Dutsen Sinai, inda Allah ya ba su dokokinsa. Daga baya, Musa ya tura mutane 12 su tafi su leƙo asirin ƙasar Kan’ana. Amma 10 daga cikinsu suka koma da mummunan labari. Suka sa mutanen suka so komawa ƙasar Masar. Domin rashin bangaskiyarsu, Allah ya yi wa Isra’ilawa horo ya sa su su yi yawo na shekara 40 cikin daji.

Daga ƙarshe, aka zaɓi Joshua ya shugabanci Isra’ilawa zuwa ƙasar Kan’ana. Domin ya taimake su su ƙwace ƙasar, Jehobah ya yi mu’ujizai. Ya sa ruwan Kogin Urdun ya daina gudu, ya sa ganuwar Jericho ta rurrushe, kuma ya sa rana ta tsaya cik na yini guda. Bayan shekara shida, suka ƙwace ƙasar daga Kan’aniyawa.

Daga Joshua alƙalai suka yi sarauta a Isra’ila na shekara 356. Za mu karanta labarin yawancinsu, har da Barak, Gideon, Jephthah, Samson, da Sama’ila. Za mu kuma karanta game da mata kamar su Rahab, Deborah, Jael, Ruth, Naomi and Delilah. Sashe na UKU ya ba da tarihi na shekaru 396.

Mazauni