MUSA ya yi dogon kiwo har dutsen Horeb domin ya nemi ciyayi ga tumakinsa. A nan sai ya ga kurmi yana cin wuta, amma ba ya ƙonewa!

Musa a wajen kurmi mai cin wuta

‘Wannan abin mamaki ne,’ ya yi tunani. ‘Bari in ɗan ratsa in gani.’ Da ya yi kusa, sai murya ta yi masa magana a cikin kurmi, tana cewa: ‘Kada ka yi kusa. Ka tuɓe takalmanka, domin kana tsaye ne a wuri mai tsarki.’ Allah ne yake magana ta bakin mala’ika, saboda haka, Musa ya rufe fuskarsa.

Sai Allah ya ce: ‘Na ga wahalar mutanena a ƙasar Masar. Saboda haka, ina so in ’yantar da su, kuma kai zan aika ka ja-goranci mutanena su fita daga ƙasar Masar.’ Jehobah zai kawo mutanensa zuwa kyakkyawar ƙasar Kan’ana.

Amma Musa ya ce: ‘Ni ba kome ba ne. Ta yaya zan yi haka? Amma a ce na tafi. Isra’ilawa za su ce mini, “Wanene ya aiko ka?” To me zan gaya musu?’

‘Haka za ka faɗa musu,’ in ji Allah. ‘ “JEHOBAH Allahn Ibrahim, Allahn Ishaku da kuma Allahn Yakubu ne ya aiko ni wurinku.” ’ Sai kuma Jehobah ya daɗa cewa: ‘Sunana ke nan har abada.’

‘Idan kuma ba su yarda da abin da na ce ba fa sa’ad da na ce da su kai ka aiko ni,’ Musa ya amsa.

‘Me ka ke riƙe da shi a hannunka?’ Allah ya tambaye shi.

Musa ya amsa: ‘Sanda ne.’

‘Ka jefar a ƙasa,’ in ji Allah. Sa’ad da Musa ya jefar, sai sandan ya zama maciji. Sai Jehobah kuma ya yi wa Musa wata mu’ujiza. Ya gaya masa: ‘ka saka hannunka cikin rigarka.’ Musa ya saka, sa’ad da ya fito da hannunsa waje, ya zama fari fat! Hannunsa ya zama kamar mai muguwar cutar nan da ake kira kuturta. Sai kuma Jehobah ya ba Musa ikon ya yi mu’ujiza ta uku. A ƙarshe ya ce: ‘Idan ka yi waɗannan mu’ujizai Isra’ilawa za su gaskata cewa ni ne na aiko ka.’

Bayan wannan sai Musa ya koma gida ya cewa Jethro: “Don Allah bari in koma in ga yadda ’yan’uwana suke a ƙasar Masar.’ Sai Jethro ya yi ban kwana da Musa, Musa ya fara tafiyarsa zuwa ƙasar Masar.

Fitowa 3:1-22; 4:1-20.Tambayoyi

 • Menene sunan wannan dutse da ke hoton nan?
 • Ka kwatanta abin mamakin da Musa ya gani sa’ad da ya je wannan dutsen da tumakinsa.
 • Menene murya ta ce daga kurmi mai cin wuta, kuma muryar wanene?
 • Yaya Musa ya amsa sa’ad da Allah ya ce masa zai ceci mutanensa daga ƙasar Masar?
 • Menene Allah ya gaya wa Musa ya ce idan mutanen suka tambaye shi wanene ya aiko shi?
 • Ta yaya Musa zai tabbatar da cewa Allah ne ya aiko shi?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Fitowa 3:1-22.

  Ta yaya labarin Musa zai ba mu tabbaci cewa idan muka ji kamar ba mu cancanci aikin da Jehobah ya ba mu ba, zai taimake mu? (Fit. 3:11, 13; 2 Kor. 3:5, 6)

 • Ka karanta 4:1-20.

  Wane canji Musa ya yi a halinsa cikin shekara 40 da ya yi a Midiya, kuma wane darasi waɗanda suke burin samun gata a ikilisiya za su koya daga wannan? (Fit. 2:11, 12; 4:10, 13; Mik. 6:8; 1 Tim. 3:1, 6, 10)

  Ko da a ce Jehobah ya yi mana horo ta ƙungiyarsa, wane tabbaci misalin Musa zai ba mu? (Fit. 4:12-14; Zab. 103:14; Ibran. 12:4-11)