Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 27: Mugun Sarki Yana Sarauta a Masar

Labari na 27: Mugun Sarki Yana Sarauta a Masar

WAƊANNAN mutanen suna tilasta wa mutanen su yi aiki. Ka ga wannan mutumin da yake yi wa wannan ma’aikacin bulala! Masu aikin daga iyalin Yakubu ne kuma ana kiransu Isra’ilawa. Kuma mutanen da suke tilasta musu su yi aiki Masarawa ne. Isra’ilawan sun zama bayin Masarawa. Ta yaya hakan ya faru?

Masarawa suna zaluntan Isra’ilawa

Babbar iyalin Yakubu ta yi zamanta lafiya na shekaru da yawa a ƙasar Masar. Yusufu mutumin da shi ne na biyun Fir’auna wajen martaba yana kula da su. Amma sa’ad da Yusufu ya mutu. Kuma sabon Fir’auna wanda ba ya son Isra’ilawan ya zama sarki a ƙasar Masar.

Saboda haka wannan mugun Fir’auna ya mayar da Isra’ilawan bayi. Kuma sai ya sa miyagun mutane su kula da su. Suka tilasta wa mutanen su yi aiki tuƙuru suna gina wa Fir’auna birane. Amma duk da haka Isra’ilawa suka ci gaba da ƙaruwa. Daga baya Masarawan suka ji tsoro cewa Isra’ilawa za su yi yawa sosai kuma su yi ƙarfi.

Masarawa suna zaluntan Isra’ilawa

Ka san abin da Fir’auna ya yi? Ya yi wa mata da suke taimakon matan Isra’ilawa sa’ad da suka haifi ’ya’ya magana, ya ce: ‘Ku kashe dukan wani yaro da aka haifa.’ Amma waɗannan matan kirki ne, suka ƙi kashe ’ya’yan.

Saboda haka Fir’auna ya ba mutanensa umurni: ‘Ku ɗauki dukan ’ya’yan Isra’ilawa maza ku kashe su. Amma kada ku kashe ’ya’ya mata.’ Wannan ba mugun umurni ba ne? Bari mu ga yadda aka ceci ɗaya daga cikin ’ya’ya mazan.

Fitowa 1:6-22.Tambayoyi

 • A wannan hoton wanene wannan mutumin da yake riƙe da bulala, kuma waye yake bugu da bulalar?
 • Bayan mutuwar Yusufu me ya sami Isra’ilawa?
 • Me ya sa Masarawa suka ji tsoron Isra’ilawa?
 • Wace doka Fir’auna ya ba wa matan da suke taimakon Isra’ilawa mata su haihu?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Fitowa 1:6-22.

  A wace hanya ce Jehobah ya fara cika alkawarinsa ga Ibrahim? (Fit. 1:7; Far. 12:2; A. M. 7:17)

  Ta yaya ungozomai Ibraniyawa suka nuna daraja da tsarkakar rai? (Fit. 1:17; Far. 9:6)

  Ta yaya aka albarkaci ungozomai domin amincinsu ga Jehobah? (Fit. 1:20, 21; Mis. 19:17)

  Ta yaya Shaiɗan ya yi ƙoƙarin ya lalata nufin Allah game da zuriya da aka yi wa Ibrahim alkawari? (Fit. 1:22; Mat. 2:16)