Yakubu da ’ya’yansa

DUBI wannan babban iyali. Waɗannan sune ’ya’yan Yakubu 12. Kuma yana da ’ya’ya mata ma. Ka san sunan ko ɗaya daga cikin waɗannan yaran. Bari mu koyi sunan wasu daga cikinsu.

Lai’atu ta haifi Reuben, Simeon, Lawi, da Yahuda. Da Rahila ta ga cewa ba ta haifi ’ya’ya ba, ta yi baƙin ciki ƙwarai. Sai ta bai wa Yakubu baiwarta Bilhah, sai Bilhah ta haifi ’ya’ya biyu masu suna Dan da Naphtali. Sai kuma Lai’atu ta bai wa Yakubu baiwarta Zilpah, sai Zilpah ta haifi Gad da Asher. Lai’atu a ƙarshe ta sake haifan ’ya’ya biyu, Issachar da Zebulun.

A ƙarshe Rahila ma ta haifi ɗa. Ya ba shi suna Yusufu. A gaba za mu koyi abubuwa da yawa game da Yusufu, domin ya zama muhimmin mutum. Waɗannan sune ’ya’ya 11 da aka haifa wa Yakubu sa’ad da yake tare da baban Rahila Laban.

Yakubu yana da wasu ’ya’ya mata, amma sunan guda ce kawai Littafi Mai Tsarki ya ba da sunanta. Sunanta Dinah.

Lokacin da Yakubu zai rabu da Laban ya koma ƙasar Kan’ana ya yi. Sai ya tara babban iyalinsa da kuma babban garkensa na tumaki da shanu, ya fara doguwar tafiyar.

Bayan Yakubu da iyalinsa sun isa Kan’ana sun ɗan daɗe, Rahila ta sake haifan wani yaro. Ta haihu ne sa’ad da suke tafiya. Rahila ta sha wuya, a ƙarshe ta mutu wurin haihuwa. Amma ɗan yaron yana lafiya. Yakubu ya sa masa suna Banyamin.

Muna so mu tuna da sunan ’ya’yan Yakubu 12 domin dukan al’ummar Isra’ila ta fito ne daga garesu. Hakika, ƙabilu 12 na Isra’ila sun sami sunansu ne daga ’ya’yan Yakubu 10 da ’ya’yan Yusufu biyu. Ishaku ya yi shakaru masu yawa bayan an haifi dukan waɗannan ’ya’yan, kuma ya yi farin ciki ƙwarai da ya sami jikoki haka masu yawa. Amma bari mu ga abin da ya faru da jikarsa Dinah.

Farawa 29:32-35; 30:1-26; 35:16-19; 37:35.Tambayoyi

 • Menene sunayen ’ya’ya maza shida na Yakubu da matarsa ta fari Lai’atu ta haifa masa?
 • Waɗanne yara maza biyu ne baiwar Lai’atu Zilpah ta haifa wa Yakubu?
 • Menene sunayen ’ya’ya maza biyu da baiwar Rahila Bilhah ta haifa wa Yakubu?
 • Waɗanne ’ya’ya maza biyu ne Rahila ta haifa, kuma menene ya faru sa’ad da ta haifi na biyun?
 • A wannan hoton, ’ya’ya maza nawa ne Yakubu yake da su, kuma me ya zo daga gare su?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Farawa 29:32-35; 30:1-26; sai kuma 35:16-19.

  Kamar yadda ya bayyana a ’ya’ya 12 na Yakubu, ta yaya Ibraniyawa na dā suke ba wa ’ya’yansu suna?

 • 2.Ka karanta Farawa 37:35.

  Ko da yake Dinah kaɗai ce aka ambata sunanta cikin Littafi Mai Tsarki, ta yaya muka sani cewa Yakubu yana da fiye da ’ya mace guda? (Far. 37:34, 35)