Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Labari na 33: Ƙetare Jar Teku

Labari na 33: Ƙetare Jar Teku

DUBI abin da yake faruwa! Wannan Musa ne da ya miƙa sandarsa bisa Jar Teku. Waɗanda suke tare da shi a wannan bangaren Isra’ilawa ne. Amma an kashe Fir’auna da duka sojojinsa a cikin teku. Bari mu ga yadda wannan ya faru.

Ruwa yana cin sojojin Masar

Kamar yadda muka koya, Fir’auna ya gaya wa Isra’ilawa su fita daga Masar bayan Allah ya kawo annoba ta goma bisa Masarawa. Wajen Isra’ilawa maza 600,000 suka fice, da kuma mata da yara. Kuma wasu mutane da yawa da suka zama masu bauta wa Jehobah suka fita tare da Isra’ilawa. Dukansu suka kwashi tumakinsu da awakinsu.

Kafin su tafi, Isra’ilawan sun roƙi Masarawa tufafi da kuma wasu abubuwa da aka yi da zinariya da azurfa. Masarawan suna tsoro domin annoba ta ƙarshe da ta zo bisa kansu. Saboda haka suka ba wa Isra’ilawa dukan abin da suka tambaya.

Bayan ’yan kwanaki Isra’ilawa suka isa bakin Jar Teku. A nan suka huta. Ana cikin haka, Fir’auna da mutanensa suka fara nadamar ƙyale Isra’ilawa su tafi. ‘Mun ƙyale bayinmu sun tafi!’ suka ce.

Sai Fir’auna ya sake canja ra’ayinsa. Ya hanzarta ya shirya karusarsa da mayaƙansa. Sai ya fara bin sawun Isra’ilawa da karusa na musamman guda 600, da kuma dukan sauran karusan Masar.

Sa’ad da Isra’ila suka ga Fir’auna da sojojinsa suna binsu, sai suka tsorata ƙwarai. Kuma babu hanyar tserewa. Gaba Jar Teku baya kuma Masarawa suna binsu. Amma sai Jehobah ya sa gajimare a tsakanin mutanensa da Masarawan. Saboda haka Masarawan ba su ga Isra’ilawan ba balle su kai musu hari.

Sai Jehobah ya gaya wa Musa ya miƙa sandarsa bisa Jar Teku. Da ya yi haka, sai Jehobah ya sa wata iska mai ƙarfi daga gabas ta busa. Sai ruwan tekun ya rabu biyu, suka yi katanga a gefensu biyu dama da hagu.

Sa’an nan Isra’ilawa suka fara tafiya a kan busasshiyar ƙasa. Ya ɗauki lokaci mai tsawo kafin dukan dukan miliyoyin mutanen suka ƙetare zuwa tsallaken tekun. A ƙarshe sai Masarawa suka ga Isra’ila. Bayinsu suna guje musu! Sai suka bi su cikin teku.

Sa’ad da suka shiga sai Allah ya sa ƙafafun kekunansu suka ɓaɓɓale. Sai Masarawan suka tsorata ƙwarai suka fara kuka suna cewa: ‘Jehobah yana yaƙi da mu a madadin Isra’ila. Mu fita daga nan!’ Amma sun maƙara.

Sa’an nan sai Jehobah ya ce wa Musa ya miƙa sandarsa bisa Jar Teku, kamar yadda ka gani a wannan hoton. Da Musa ya yi haka, sai katangar ruwa ta rushe a kan Masarawan da karusansu. Dukan sojojin sun bi Isra’ilawa cikin tekun. Kuma babu ko ɗaya daga cikinsu da ya tsira da ransa!

Mutanen Allah sun yi farin ciki sosai domin ya cece su! Saboda haka mazan suka rera waƙar godiya ga Jehobah, suna cewa: ‘Jehobah ya ci gawurtacciyar nasara. Ya jefa dawakai da mahayansu cikin teku.’ Maryamu yayar Musa ta ɗauki tambari, sai dukan matan suka bi ta da nasu tamburan. Sa’ad da suke rawa suke murna, suna rera waƙar da mazan suke rerawa: ‘Jehobah ya ci gawurcacciyar nasara. Ya jefa dawakai da mahayansu cikin teku.’

Fitowa surori 12 zuwa 15.Tambayoyi

 • Isra’ilawa maza da mata da yara nawa ne suka bar ƙasar Masar, kuma su waye suka bi su?
 • Yaya Fir’auna ya ji da ya ƙyale Isra’ilawa su tafi, kuma menene ya yi?
 • Menene Jehobah ya yi don ya hana Masarawa kai wa mutanensa hari?
 • Menene ya faru sa’ad Musa ya miƙa sandansa bisa Jar Teku, kuma menene Isra’ilawa suka yi?
 • Menene ya faru sa’ad da Masarawa suka bi Isra’ilawa cikin teku?
 • Ta yaya Isra’ilawa suka nuna cewa suna farin ciki kuma suna godiya ga Jehobah domin sun tsira?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Fitowa 12:33-36.

  Ta yaya ne Jehobah ya sa aka biya Mutanensa domin duka shekaru da suka yi suna bauta wa Masarawa? (Fit. 3:21, 22; 12:35, 36)

 • Ka karanta Fitowa 14:1-31.

  Ta yaya ne kalmomin Musa da aka rubuta a Fitowa 14:13, 14 suka shafi bayin Jehobah a yau yayin da suke sauraran yaƙin Armageddon? (2 Laba. 20:17; Zab. 91:8)

 • Ka karanta Fitowa 15:1-8, 20, 21.

  Me ya sa bayin Jehobah za su rera masa waƙar yabo? (Fit. 15: 1, 2; Zab. 105:2, 3; R. Yoh. 15:3, 4)

  Wane misali ne na yabon Jehobah Maryamu da sauran mata a Jar Teku suka kafa wa mata Kiristoci a yau? (Fit. 15:20, 21; Zab. 68:11)