YUSUFU ya kasa jimrewa. Ya sallami dukan bayinsa daga ɗakin. Sa’ad da ya kaɗaita da ’yan’uwansa, Yusufu ya fara kuka. Ba za mu iya ma tunanin mamakin da ’yan’uwansa suka yi ba, domin ba su san abin da ya sa yake kuka ba. A ƙarshe ya gaya musu: ‘Ni ne Yusufu. Babana yana raye kuwa?’

’Yan’uwansa suka yi ta mamaki har suka kasa magana. Suna tsoro. Amma Yusufu ya gaya musu: ‘Don Allah ku matso kusa.’ Da suka matso, sai ya ce: ‘Ni ɗan’uwanku ne Yusufu, wanda kuka sayar zuwa ƙasar Masar.’

Yusufu ya ci gaba da yi musu magana cikin hankali: ‘Kada ku ga laifin juna domin kun sayar da ni zuwa nan. Ainihi Allah ne ya aiko ni Masar domin in ceci rayukan mutane. Fir’auna ya naɗa ni mai sarautar dukan ƙasar. Saboda haka yanzu ku hanzarta ku gaya wa babana wannan. Kuma ku gaya masa ya zo ya zauna a nan.’

Yusufu ya rungumi ’yan’uwansa kuma ya sumbace su duka. Sa’ad da Fir’auna ya ji cewa ’yan’uwan Yusufu sun zo, ya gaya wa Yusufu: ‘Bari su ɗauki kekuna su tafi su kawo ubansu da iyalansu su dawo nan da zama. Zan ba su wuri mafi kyau a cikin dukan ƙasar Masar.’

Haka kuwa suka yi. A nan kana iya ganin Yusufu ya haɗu da babansa sa’ad da ya zo ƙasar Masar da dukan iyalinsa.

Iyalin Yakubu ta girma ƙwarai. Su 70 ne sa’ad da suka ƙaura zuwa ƙasar Masar, idan aka haɗa Yakubu da ’ya’yansa da jikokinsa. Amma kuma wannan ya haɗa da matansu da kuma wataƙila bayi masu yawa. Dukan waɗannan suka koma da zama a ƙasar Masar. Aka fara kiransu Isra’ilawa domin Allah ya canja wa Yakubu suna zuwa Isra’ila. Isra’ilawa suka zama mutane na musamman ga Allah, kamar yadda za mu gani a gaba.

Farawa 45:1-28; 46:1-27.

Yusufu da iyalinsa


Tambayoyi

 • Menene ya faru sa’ad da Yusufu ya gaya wa ’yan’uwansa shi Yusufu ne?
 • Wane bayani Yusufu ya yi wa ’yan’uwansa?
 • Menene Fir’auna ya ce sa’ad da ya sami labarin ’yan’uwan Yusufu?
 • Yaya girman iyalin Yakubu sa’ad da suka ƙaura zuwa ƙasar Masar?
 • Me aka koma kiran iyalin Yakubu kuma me ya sa?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Farawa 45:1-28.

  Ta yaya labarin Yusufu a cikin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah zai iya canja niyyar cutar da bayinsa zuwa albarka? (Far. 45:5-8; Isha. 8:10; Filib. 1:12-14)

 • Ka karanta Farawa 45:1-28.

  Wane tabbaci Jehobah ya bai wa Yakubu a hanyarsa ta zuwa ƙasar Masar? (Far. 46:1-4)