In kana da abokin da kake ƙaunarsa kuma kana daraja shi, za ka yi ƙoƙari ka zama kamarsa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji nagari ne mai adalci.” (Zabura 25:8) Don mu zama aminan Allah, dole ne mu zama mutane nagargaru masu adalci. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku zama fa masu koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu; ku yi tafiya cikin ƙauna.” (Afisawa 5:1, 2) Ga wasu hanyoyi da za a yi haka:

Ka taimaka wa wasu. “Bari mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane.”—Galatiyawa 6:10.

Ka yi aiki da ƙwazo. “Mai-yin sata kada shi ƙara yin sata: amma gwamma shi yi aiki, da hannuwansa yana aika abin da ya ke da kyau.”—Afisawa 4:28.

Ka tsabtace jikinka da kuma ɗabi’arka. “Bari mu tsarkake kanmu daga dukan ƙazantar jiki da ta ruhu, muna kāmala tsarki cikin tsoron Allah.”—2 Korintiyawa 7:1.

 Ka ƙaunaci iyalinka kuma ka daraja su. “Kowane ɗayanku shi yi ƙaunar matatasa kamar kansa; matan kuma ta ga ƙwarjinin mijinta. Ku ’ya’ya, ku yi biyayya da waɗanda suka haife ku.”—Afisawa 5:33–6:1.

Ka ƙaunaci wasu. “Mu yi ƙaunar junanmu: gama ƙauna ta Allah ce.”—1 Yohanna 4:7.

Ka bi dokar ƙasa. “Bari kowane mai rai shi yi zaman biyayya da ikon [gwamnati] . . . Ku ba kowa hakinsa: gandu ga wanda gandu ya wajaba.”—Romawa 13:1, 7.