Za ka iya koya game da Jehobah ta wurin karatun Littafi Mai Tsarki. Dā can, Allah ya zaɓi wasu mutane su rubuta nufinsa. Waɗannan rubuce-rubuce ne ake kira Littafi Mai Tsarki. A yau muna koya game da Allah ta wurin karatun Littafi Mai Tsarki. Domin Littafi Mai Tsarki ya ƙunshi kalmomin Jehobah, ko kuma saƙo, ana kiransa Kalmar Allah. Za mu iya gaskata abin da Littafi Mai Tsarki ya ce saboda Jehobah ba zai yi ƙarya ba. “Ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya.” (Ibraniyawa 6:18) Kalmar Allah tana ɗauke da gaskiya.—Yohanna 17:17.

Littafi Mai Tsarki yana ɗaya daga cikin kyauta mai tamani da Allah ya ba mu. Yana kama da wasiƙa daga uba zuwa ga yaransa da yake ƙauna. Ya gaya mana game da alkawari da Allah ya yi na canja duniya zuwa wurin zama mai kyau—aljanna. Ya gaya mana abin da ya yi a dā, abin da yake yi yanzu, da kuma abin da zai yi a nan gaba ga yaransa masu aminci. Yana kuma taimakonmu mu magance  damuwa da muke da su da kuma yadda za mu sami farin ciki.—2 Timotawus 3:16, 17.

Shaidun Jehobah aminan Allah ne; za su taimake ka ka fahimci abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Ka gaya musu cewa kana son ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Ba sa karɓan kuɗi don wannan. (Matta 10:8) Ƙari ga haka, za ka iya halartan taro na Kirista, waɗanda ake yi a wuraren sujjada da ake kira Majami’ar Mulki. Idan kana halartan taro na Kirista, zai yi maka sauƙi ka daɗa sanin Allah.

Za ka iya koya game da Allah daga abubuwa da ya yi. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “A cikin farko Allah ya halitta sama da ƙasa.” (Farawa 1:1) Lokacin da Jehobah ya halicci “sama,” ya yi rana. To menene wannan ya gaya mana game da Allah? Ya gaya mana cewa Jehobah yana da iko sosai. Shi ne kaɗai zai iya halittan abu mai ƙarfi kamar rana. Ya kuma gaya mana cewa Jehobah yana da hikima, tun da ana bukatar hikima don a yi rana, da take ba da zafi da haske kuma ba ta ƙarewa.

Abin da Jehobah ya halitta ya nuna cewa yana ƙaunarmu. Ka yi tunanin dukan ’ya’yan itatuwa dabam-dabam da suke wannan duniyar. Da Jehobah zai yi guda ɗaya ne kawai saboda mu—ko ma ba zai yi ba sam sam. Maimakon haka, Jehobah ya ba mu ’ya’yan itatuwa dabam-dabam a siffa dabam-dabam, girmansu, launinsu, da kuma ɗanɗanonsu dabam-dabam. Wannan ya nuna cewa Jehobah Allah ne mai ƙauna, kuma ƙari ga haka, yana da karimci da alheri.—Zabura 104:24.