Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 SASHE NA 7

Wane Ne Yesu?

Wane Ne Yesu?

Jehobah ya aiko Yesu zuwa duniya. 1 Yohanna 4:9

Idan muna son mu faranta wa Jehobah rai, dole ne mu saurari wani mutum mai muhimmanci. Shekaru aru-aru kafin a halicci Adamu, Jehobah ya halicci wani mala’ika mai girma a sammai.

Daga baya, Jehobah ya sa wata budurwa mai suna Maryamu ta haife shi a Baitalami. An sa wa yaron suna Yesu.—Yohanna 6:38.

A matsayin mutum a duniya, Yesu ya nuna halayen Allah. Ya nuna alheri, ƙauna, kuma mutane ba sa gudunsa. Ya koya wa mutane gaskiya game da Jehobah da gaba gaɗi.

 Yesu ya aikata nagarta amma an ƙi jininsa. 1 Bitrus 2:21-24

Yesu ya kuma warkar da marasa lafiya kuma ya ta da wasu da suka mutu.

Shugabannin addinai sun ƙi jinin Yesu domin ya fallasa koyarwarsu ta ƙarya da kuma mugun halayensu.

Shugabannin addinai sun lallashi Romawa su bugi Yesu kuma su kashe shi.