Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada

 SASHE NA 12

Ta Yaya Za Ka Iya Samun Iyali Mai Farin Ciki?

Ta Yaya Za Ka Iya Samun Iyali Mai Farin Ciki?

Kana bukatar ka nuna ƙauna idan kana son ka samu iyali mai farin ciki. Afisawa 5:33

Mizanin Allah shi ne aure ya kasance tsakanin namiji ɗaya da mace guda.

Miji mai ƙauna zai bi da matarsa cikin ƙauna da fahimi.

Ya kamata mata ta ba da haɗin kai ga mijinta.

Yara suna bukatar su yi biyayya ga iyayensu.

 Ka kasance mai alheri da aminci, ba azzalumi ko marar aminci ba. Kolosiyawa 3:5, 8-10

Kalmar Allah ta ce miji ya ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar jikinsa kuma mace ta ga ƙwarjinin mijinta.

Yin jima’i da wadda mutum bai aura ba zunubi ne. Auren mace fiye da guda zunubi ne.

Kalmar Jehobah tana koya wa iyalai yadda za su yi farin ciki.