Sa’ad da muka karanta Littafi Mai Tsarki, kamar dai Allah yana yi mana magana ne. 2 Timotawus 3:16

Allah na gaskiya ya ja-goranci mazaje su rubuta nufinsa a cikin wani littafi na musamman. Wannan littafin shi ne Littafi Mai Tsarki. Yana ɗauke da saƙo masu muhimmanci da Allah yake son ka sani.

Allah ya san abin da ya fi dacewa da mu kuma shi ne Tushen dukan hikima. Idan ka saurare shi, za ka kasance da hikima sosai. —Misalai 1:5.

Allah yana son kowane mutum a duniya ya karanta Littafi Mai Tsarki. Za a iya samunsa a harsuna masu yawa a yau.

Idan kana son ka ji abin da Allah yake cewa, dole ne ka karanta Littafi Mai Tsarki kuma ka fahimce shi.

 Mutane a ko’ina a duniya suna koyo game da Allah. Matta 28:19

Shaidun Jehobah za su iya taimaka maka ka fahimci Littafi Mai Tsarki.

Suna koyar da gaskiya game da Allah a dukan duniya.

Ba ka bukatar ka biya ko sisi don samun wannan koyarwar. Kana kuma iya samun koyarwa game da Allah a Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah da ke yankinku.