Yawancin mutane a zamanin Nuhu sun yi abin da bai da kyau. Farawa 6:5

Adamu da Hauwa’u sun haifi ’ya’ya, kuma mutane sun yi yawa a duniya. Bayan wani lokaci, wasu mala’iku suka yi tawaye kamar Shaiɗan.

Sun zo duniya kuma suka zama mutane domin su auri mata. Matan sun haifi ’ya’ya maza ƙatta masu mugun fushi da ƙarfi.

Duniyar ta cika da mutanen da ke aikata abubuwa marar kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce “muguntar mutum ta yi yawa cikin duniya, kuma kowacce shawara ta tunanin zuciyarsa mugunta ce kaɗai kullayaumi.”

 Nuhu ya saurari Allah kuma ya gina jirgin. Farawa 6:13, 14, 18, 19, 22

Nuhu mutumi ne mai aminci. Jehobah ya gaya wa Nuhu cewa, zai halaka mugayen mutane da babbar rigyawa.

Allah ya kuma gaya wa Nuhu cewa ya gina jirgin ruwa mai girma, kuma ya shigar da iyalinsa da kowace irin dabba a cikinsa.

Nuhu ya gargaɗi mutane game da Rigyawar da ke tafe, amma ba su saurare shi ba. Wasu sun yi ma Nuhu dariya; wasu kuma sun tsane shi.

Sa’ad da aka gama gina jirgin, Nuhu ya shigar da dabbobi cikin jirgin.