Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada

 SASHE NA 14

Ta Yaya Za Ka Kasance da Aminci ga Jehobah?

Ta Yaya Za Ka Kasance da Aminci ga Jehobah?

Ka bi Allah. 1 Bitrus 5:6-9

Ka guji saka hannu a duk wasu al’adun da ba su jitu da Littafi Mai Tsarki ba. Kana bukatar gaba gaɗi don ka yi hakan.

Kada ka shiga siyasar wannan duniyar; ba sa goyon bayan Jehobah da Mulkinsa.

 Ka yi zaɓi mai kyau, wato, ka saurari Allah. Matta 7:24, 25

Ka yi tarayya da Shaidun Jehobah; za su taimake ka ka kusaci Allah.

Ka ci gaba da koya game da Allah kuma ka ƙoƙarta ka yi biyayya da dokokinsa.

Sa’ad da bangaskiyarka ta yi ƙarfi, ka keɓe kanka ga Jehobah kuma ka yi baftisma.—Matta 28:19.

Ka saurari Allah. Ka karanta Littafi Mai Tsarki, kuma ka tambayi Shaidun Jehobah su taimake ka ka fahimce shi. Ka yi amfani da abin da ka koya. Idan ka yi haka, za ka rayu har abada.—Zabura 37:29.