Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada

 SASHE NA 2

Wane Ne Allah Na Gaskiya?

Wane Ne Allah Na Gaskiya?

Allah na gaskiya guda ɗaya ne tak, kuma sunansa Jehobah. (Zabura 83:18) Yana zaune ne a sama; ba ma iya ganinsa. Yana ƙaunarmu, kuma yana so mu ƙaunace shi. Yana kuma so mu ƙaunaci mutane. (Matta 22:35-40) Shi ne Maɗaukaki Duka, Mahaliccin dukan abubuwa.

Farkon halittar Allah shi ne wani ruhu mai iko wanda daga baya a duniya aka san shi da sunan nan Yesu Kristi. Jehobah ya kuma halicci mala’iku.

Jehobah ne ya halicci dukan abubuwan da ke sama . . .da ƙasa. Ru’ya ta Yohanna 4:11

 Jehobah ne ya halicci taurari da duniya da kuma dukan abubuwan da ke cikinta.—Farawa 1:1.

Shi ne ya sifanta Adamu, mutumi na farko, daga turɓayar ƙasa.—Farawa 2:7.