Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada

 SASHE NA 9

A Yaushe Ne Duniya Za ta Zama Aljanna?

A Yaushe Ne Duniya Za ta Zama Aljanna?

Matsalolin da ke faruwa a duniya sun tabbatar da cewa Mulkin Allah zai ɗauki mataki ba da daɗewa ba. Luka 21:10, 11; 2 Timotawus 3:1-5

Littafi Mai Tsarki ya annabta abubuwa da yawa da suke faruwa a yau. Ya ce mutane za su zama masu son kuɗi, marasa bin iyaye, masu zafin hali, da masu son annashuwa.

Za a yi manyan girgizar ƙasa, yaƙe-yaƙe, ƙarancin abinci, da cuta a wurare dabam-dabam. Waɗannan abubuwan suna faruwa a yau.

Yesu ya ce za a yi wa’azin bisharar Mulki a dukan duniya.—Matta 24:14.

 Mulkin zai cire dukan mugunta. 2 Bitrus 3:13

Ba da daɗewa ba, Jehobah zai halaka dukan mugaye.

Za a hukunta Shaiɗan da aljanu.

Waɗanda suka saurari Allah za su shiga sabuwar duniya, inda mutane za su amince da juna kuma su ƙaunaci juna, kuma jin tsoro zai zama tsohon labari.