Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  Yuni 2017

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | IRMIYA 51-52

Maganar Jehobah Tana Cika a Koyaushe

Maganar Jehobah Tana Cika a Koyaushe

Jehobah ya annabta abin da zai faru a nan gaba

Maharbin da ke tsaron fādar Fasiya

“Ku tsinana kibawu”

51:11, 28

  • Mutanen Midiya da Fasiya ƙwararrun maharba ne kuma kibiya ce ainihin makaminsu. Don haka, sun watsa kibawunsu don su yi tsini sosai

Sojojin “Babila sun ƙi yaƙi”

51:30

  • Allon Nabonidus Chronicle ya ce: “Sojojin Sairus sun halaka Babila ba tare da yin yaƙi ba.” Ba su yi yaƙin fito-na-fito ba kuma hakan ya jitu da annabcin Irmiya

Allon Nabonidus Chronicle

‘Babila za ta zama tullan ƙasa da kuma kango har abada’

51:37, 62

  • Ɗaukakar Babila ta soma ragewa a shekara ta 539. Iskandari Mai Girma ya so ya mai da Babila babban birninsa, amma ya mutu babu zato. A lokacin da aka fara samun Kiristoci, da akwai wasu Yahudawa da suke zama a Babila kuma hakan ne ya sa Bitrus ya je wajen. Amma a ƙarni na huɗu, mutane sun daina zama a ƙasar gabaki ɗaya

Waɗanne matakai ne ya kamata in ɗauka don annabcin Littafi Mai Tsarki da suke cika?

 

Mene ne zan iya koya wa wasu game da annabcin nan?