Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 RAYUWAR KIRISTA

Ka Gaskata da Alkawuran Jehobah Kuwa?

Ka Gaskata da Alkawuran Jehobah Kuwa?

Joshua da Sulemanu sun shaida cewa Jehobah yana cika dukan alkawuransa. (Jos 23:14; 1Sa 8:56) Abin da mutanen nan biyu suka shaida zai ƙarfafa bangaskiyarmu sosai.​—2Ko 13:1; Tit 1:2.

Ta yaya Jehobah ya cika alkawuransa a zamanin Joshua? Don Allah, ku da iyalinku ku kalli wasan kwaikwayon nan ‘Babu Kalmar Allah da Ba Ta Tabbata Ba.’ Sa’an nan ku amsa tambayoyin nan: (1) Ta yaya za ka iya yin koyi da bangaskiyar Rahab? (Ibr 11:31; Yaƙ 2:​24-26) (2) Ta yaya misalin Achan ya nuna cewa yin rashin biyayya da gangan bai dace ba? (3) Me ya sa Gibeyonawa suka yi wa Joshua ƙarya kuma suka sasanta da Isra’ila duk da cewa su jarumai ne? (4) Ta yaya maganar Jehobah ta cika sa’ad da sarakuna biyar na Amoriyawa suka kai wa Isra’ila hari? (Jos 10:​5-14) (5) Ta yaya Jehobah ya taimaka maka domin ka biɗi Mulkin Allah da adalcinsa farko a rayuwarka?​—Mt 6:33.

Bangaskiyarmu za ta ƙara ƙarfi idan muka ci gaba da yin tunani a kan abubuwan da Jehobah ya yi a dā da waɗanda yake yi yanzu da kuma waɗanda zai yi a nan gaba.​—Ro 8:​31, 32.

Shin kana da bangaskiya kamar Joshua?