Jehobah ya ba Ezekiyel takarda a wahayi kuma ya ce ya ci takardar. Mene ne ma’anar wahayin?

2:9–3:2

  • Ya kamata Ezekiyel ya fahimci Kalmar Allah sosai. Yin bimbini a kan kalmomin da ke cikin littafin zai sosa zuciyarsa kuma zai motsa shi ya yi magana

3:3

  • Takardar da Ezekiyel ya ci tana da zaƙi domin ya kasance da ra’ayi mai kyau game da aikinsa

Ta yaya addu’a da nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini za su taimaka mini?

 

Ta yaya zan kasance da ra’ayi mai kyau game da yin wa’azi?