AWAKE!

Tambaya: Shin Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne? Ko kuma littafin ne da ke ɗauke da ra’ayin mutane?

Nassi: 2Ti 3:16

Abin da Za Ka Ce: Wannan mujallar Awake! ta ambata dalilai uku da suka nuna cewa Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne.

KU KOYAR DA GASKIYA

Tambaya: Yaya ya kamata mu ɗauki rai da aka ba mu kyauta?

Nassi: R. Yoh 4:11

Gaskiya: Tun da Allah ne ya ba mu rai, ya kamata mu riƙa daraja rai da ya ba mu. Don haka, mu riƙa kula da kanmu sosai kuma kada mu kashe wani. Mu riƙa ɗaukan rai da daraja sosai.

MENE NE KE KAWO FARIN CIKI A IYALI?

Tambaya: Ka lura da tambayar da ke gaban wannan warƙar da kuma amsoshin da aka bayar. Mene ne ra’ayinka?

Nassi: Lu 11:28

Abin da Za Ka Ce: Wannan warƙar ta ambata abubuwan da za su amfani iyalinka da kuma dalilin da ya sa za mu iya gaskata da Littafi Mai Tsarki.

KA RUBUTA TAKA GABATARWA

Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.