Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  Yuli 2017

 RAYUWAR KIRISTA

Abubuwan da Bai Kamata a Yi Ba a Wa’azi

Abubuwan da Bai Kamata a Yi Ba a Wa’azi

Kiristoci ‘abin kallo ne ga duniya.’ (1Ko 4:⁠9) Saboda haka, zai yiwu cewa wasu suna leƙen mu daga wundon gidansu ko kuma suna ɓoyewa a bayan ƙofarsu don su ji hirar da muke yi. Zai ma iya yiwu cewa gidan na da kyamara ko abin ɗaukan magana. Ga wasu abubuwa da bai kamata mu yi ba sa’ad da muka shiga gidan mutane.​—2Ko 6:3.

ƊABI’ARMU (Fib 1:27):

  • Bai kamata mu leƙa gidan mutum ba. Bai kuma kamata mu ci abinci ko mu sha ruwa ko lemu ko kuma mu riƙa yin waya da aika saƙonni ba sa’ad da muke tsaye a bakin ƙofar mutum

FURUCINMU (Afi 4:29):

  • Sa’ad da kake bakin ƙofar mutum, kada ka faɗi abin da ba za ka so maigidan ya ji ba. Wasu ’yan’uwa ma suna daina hira gabaki ɗaya sa’ad da suke bakin ƙofa don su yi tunani a kan abin da za su gaya wa maigidan

A waɗanne hanyoyi ne kuma za ka iya nuna halaye masu kyau a bakin ƙofar mutum?