Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 60-68

Ku Yabi Jehobah Mai Jin Addu’a

Ku Yabi Jehobah Mai Jin Addu’a

Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka cika alkawuranka

61:1, 8

  • Idan muna ambata alkawuranmu a addu’a, hakan zai sa mu yi ƙoƙari mu cika su

  • Wa’adin da muka yi na bauta wa Allah shi ne alkawarin da ya fi muhimmanci

Hannatu

Ka nuna ka dogara ga Jehobah ta wurin gaya masa damuwarka

62:8

  • Addu’a mai kyau ita ce wadda za ka gaya wa Jehobah duk abin da ke zuciyarka

  • Idan muka gaya wa Jehobah abin da muke bukata, za mu gane idan ya amsa mana

Yesu

Jehobah yana jin addu’ar dukan waɗanda suke masa biyayya

65:1, 2

  • Jehobah yana jin addu’o’in “dukan masu rai” da suke so su san shi kuma su bauta masa

  • Za mu iya yin addu’a ga Jehobah a kowane lokaci

Karniliyus

Abubuwan da nake so in gaya wa Jehobah a addu’a.