• Waƙa ta 104 da Addu’a

 • Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

 • Ku Yabi Jehobah Mai Jin Addu’a”: (minti 10)

  • Za 61:1, 8—Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka cika alkawuranka (w99 9/15 9 sakin layi na 1-4)

  • Za 62:8—Ka nuna ka dogara ga Jehobah ta wajen gaya masa damuwarka (w15 4/15 25-26 sakin layi na 6-9)

  • Za 65:1, 2—Jehobah yana jin addu’ar dukan waɗanda suke masa biyayya (w15 4/15 22 sakin layi na 13-14; w10 4/15 5 sakin layi na 10; it-2 668 sakin layi na 2)

 • Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)

  • Za 63:3—Me ya sa rahamar Jehobah ta fi rai? (w06 7/1 20 sakin layi na 9)

  • Za 68:18—Su waye ne “kyautai a wurin mutane”? (w06 7/1 19 sakin layi na 12)

  • Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya mini game da Jehobah?

  • Waɗanne darussa ne na koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon da zan iya yin amfani da su a wa’azi?

 • Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Za 63:1–64:10

KA YI WA’AZI DA ƘWAZO

 • Ka Shirya Gabatarwa na Wannan Watan: (minti 15) Tattaunawa. Ka saka bidiyon gabatarwar mujallu, sai ka tattauna wasu abubuwa a ciki. Ka ƙarfafa masu shela su rubuta tasu gabatarwa.

RAYUWAR KIRISTA

 • Waƙa ta 81

 • Sauƙaƙa Rayuwarmu Zai Sa Mu Yabi Allah”: (minti 15) Ka soma da tattauna talifin. Bayan haka, sai ka saka da kuma ɗan tattauna bidiyon nan Muna Rayuwa Mai Sauƙi da ke jw.org. Ka ƙarfafa ’yan’uwa su yi la’akari da hanyoyin da za su iya sauƙaƙa rayuwarsu don su iya kyautata hidimarsu ga Jehobah.

 • Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) ia babi na 19 sakin layi na 1-16

 • Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)

 • Waƙa ta 88 da Addu’a