Yesu shi ne mutum mafi girma da ya taɓa rayuwa a duniya. Duk da haka, ya ɗaukaka Jehobah ta wajen kasancewa da sauƙin kai. (Yoh 7:​16-18) Amma Shaiɗan ya zama Iblis wanda yake nufin “Maƙaryaci.” (Yoh 8:​44, Littafi Mai Tsarki) Kamar Shaiɗan, Farisawa sun nuna girman kai, shi ya sa ba sa daraja waɗanda suka gaskata da Almasihu. (Yoh 7:​45-49) Ta yaya za mu yi koyi da Yesu sa’ad da muka sami wata gata a ikilisiya?

KU KALLI BIDIYON NAN “KU ƘAUNACI JUNA”​—KU GUJI YIN KISHI DA BURGA, SASHE NA 1, SAI KU TATTAUNA TAMBAYAR NAN:

  • Me ya nuna cewa Alex yana da girma kai?

KU KALLI BIDIYON NAN “KU ƘAUNACI JUNA”​—KU GUJI YIN KISHI DA BURGA, SASHE NA 2, SAI KU TATTAUNA TAMBAYOYIN NAN:

  • Ta yaya Alex ya kasance da sauƙin kai?

    Ta yaya Alex ya ƙarfafa Bill da kuma Carl?

KU KALLI BIDIYON NAN “KU ƘAUNACI JUNA”​—KU TSANI FAHARIYA DA RASHIN HANKALI, SASHE NA 1, SAI KU TATTAUNA TAMBAYAR NAN:

  • Me ya nuna cewa Ɗan’uwa Harris bai nuna sauƙin kai ba?

KU KALLI BIDIYON NAN “KU ƘAUNACI JUNA”​—KU TSANI FAHARIYA DA RASHIN HANKALI, SASHE NA 2, SAI KU TATTAUNA TAMBAYOYIN NAN:

  • Ta yaya Ɗan’uwa Harris ya nuna sauƙin kai?

    Me ’Yar’uwa Faye ta koya daga halin da Ɗan’uwa Harris ya nuna?