6:9-11, 25-27, 54, 66-69

Sa’ad da Yesu ya yi wani kwatanci da almajiransa ba su fahimta ba, wasu ba su ji daɗi ba. Sai suka daina bin sa. Tun da Yesu ya ciyar da su ta hanyar mu’ujiza kuma sun tabbata cewa ikon da ya yi amfani da shi daga Allah ne, me ya sa suka daina bin sa? Ba sa bin sa da niyya mai kyau. Suna bin Yesu don abubuwan da suke samu a wurinsa ne.

Don haka, ya kamata mu tambayi kanmu: ‘Me ya sa nake bin Yesu? Ina yin hakan don albarkun da nake samuwa yanzu da waɗanda zan samu a nan gaba ne? Ko kuma ina yi ne domin ina ƙaunar Jehobah kuma ina son in faranta masa rai?’

Me ya sa za mu iya daina bauta wa Jehobah idan muna bauta masa musamman don dalilai na gaba?

  • Muna jin daɗin yin tarayya da mutanen Allah

  • Muna son mu yi rayuwa a Aljanna